✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babban Alkalin Najeriya bai Kamu da COVID-19 ba —Kotun Koli

Ta kalubalanci masu ikirarin da su kawo sakamakon gwajin da ke nuna hakan

Kotun Koli ta Najeriya ta karyata rahoton da ke cewa Babban Alkalin Najeriya (CJN) , Mai Shari’a Tanko Muhammad (SAN) ya kamu da cutar COVID-19.

Kotun Koli ta musanta rahoton da ya ambato wani Alkali a Kotun Kolin na sanar da haka a Abuja a hedikwatan Kungiyar Lauyoyi Musulmai ta Najeriya (MULAN) a Abuja.

Sai dai Daraktan Yada Labaran Kotun Kolin, Festus Akande, a cikin wata sanarwa ya ce babu wata takardar asibiti da ke nuna CJN Tanko Muhammad ya harbu da COVID-19.

“Masu yada labarin su kara bincikawa daga majiyar tasu su kuma samo sakamakon gwajin da ke tabbatar da karyar tasu.

“Zuwa yanzu, babu wanda ya kawo min ko ya kawo wa wani a Kotun Koli sakamakon gwajin da suke ambata a rahoton”, inji Akande.

Mai Shari’a Tanko Muhammad dai bai halarci taron rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya (SAN) 72 ba, da aka yi a Kotun Kolin ranar Litinin.

Rashinsa a taron na shiga Sabuwar Shekarar Kotun Kolin ya sa mai bi masa, Mai Shari’a Olabode Rhodes-Vivour ta jagoranci bikin da kuma rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin su 72.

Rashin halartarsa a taron da bisa al’ada shi ne zai jagoranta, ta sa ake nuna damuwa game da lafiyar CJN Tanko Muhammad wanda ke jinya a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Sai dai Daraktan Yada Labaran Kotun Kolin, Festus Akande, ya ce babu kanshin gaskiya a labarin da ake yadawa game da lafiyar Mai Shari’a Tanko Muhammad.

“Daya karyar ita ce ikirarin cewa CJN din ya shafe makonni ba tare an gan shi ba a bainar jama’a.

“Muna mamakin inda dan jaradar ya samu wannan bayani, domin CJN ya yi ta gudanar da harkokinsa, har ya rantsar da sabbin Alkalan Kotun Koli a makonnin baya”, inji sanarwar.