✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Chinedu Ikedieze ne babban jarumin fim din ‘Hajiya Babba’

Fitaccen jarumin fina-finan barkwancin Kudancin Najeriya Chinedu Ikedieze wanda aka fi sani da Aki ne babban jarumin fim din ‘Hajiya Babba’.Kamfanin Barumi Mobies ne ya…

Fitaccen jarumin fina-finan barkwancin Kudancin Najeriya Chinedu Ikedieze wanda aka fi sani da Aki ne babban jarumin fim din ‘Hajiya Babba’.
Kamfanin Barumi Mobies ne ya shirya fim din ‘Hajiya Babba’, inda Ilyasu Umar (Tantiri) ya ba da umarni. Yakubu M Kumo ne ya tsara labarin fim din.
An kammala daukar fim din a Abuja, sannan masu sharhi sun ce fim din ya zo da sabon salon barkwanci a masana’antar fina-finan Hausa.
Jarumin ya ce ya yi farin ciki da ya kasance babban jarumin a fim din Hausa ‘Hajiya Babba’.
“Na yi farin ciki da na kasance babban jarumi a fim din ‘Hajiya Babba’, a wancan fim din da na yi (karangiya), ba ni ba ne babban jarumi. Yadda na yi a fim din ya sanya suka ga dacewar su ci gaba da sanya ni a fim dinsu, wanda ga shi yanzu na zama babban jarumi.” Inji Aki.
Ya ce a fim din baya na Hausa da  ya yi ya sha wahala, amma a yanzu al’amarin ya zo masa da sauki, kasancewar a wancan lokacin shi ne karo na farko.
Sauran ’yan wasan da suka taka rawa a fim din sun hada da  Rabilu Musa (Ibro) da Hafsat Sharada (Mai Aya) da Sani Garba Sk da Binta Soro da sauransu.