✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ICC za ta binciki Rasha kan mamaye Ukraine

EU ta kwace kadarorin Putin da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergie Lavrov

Tarayyar Turai (EU) ta yi ittifakin kwace kadarorin Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin da Ministan Harkokin Wajen kasar, Sergiy Lavrov, saboda yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine.

An kuma dauke gudanar da wasan karshen gasar Zakarun Turai da aka shirya gudanarwa a birnin St. Petersburg na kasar Rasha zuwa birnin Paris na kasar Faransa.

Wadannan na daga cikin karin matakan da kasashen duniya suke dauka da zummar karya tattalin arzikin Rasha na tsawon lokaci.

Tuni dai aka fara gwabza kazamin fada tsakanin dakarun Rahsa da na Ukraine, inda Rasha ke son yi wa Kiev, babban birnin kasar ta Ukraine kawanya.

Dakarun Rasha sun ci gaba da yi wa Ukraine luguden wuta ta sama da kasa da kuma teku, ta yankin Gabashi da Arewaci da kuma Kudanci, ciki har da birni na biyu mafi girma a kasar, wato Khakhiv.

Wasu majiyoyi sun ce duk da haka, sojojin na Rasha sun fuskanci turjiya daga mayakan yankin Crimea, fiye da yadda suka yi hasashe, wanda hakan ke kawo musu tafiyar hawainiya a manufartu da isa birnin Kiev.

Kazalika rahotanni sun ce har yanzu Rasha ba ta kwace ikon sararin samaniyar Ukraine ba, kamar yadda Rashar ta yi ikirari da farko.

Za a hukunta Rasha

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ce za ta binciki Rasha kan zargin aikata laifukan yaki da tauye hakkin dan Adam a mamayar ta Rasha a Ukraine.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin zai raba akalla mutum miliyan biyar da gidajensu a Ukraine.

Ta fara shirin tura tallafin Dala miliya 20 na kayan agaji ga Ukraine a yayin da EU ta ware Dala biliyan 1.7 domin tallafa wa tattalin arzikin kasar.

Kasa da awa 24 da fara yakin da Rasha da kaddamar, Gwamnatin Ukraine ta ’yan kasarta akalla 100,000 sun rasa matsugunansu.

Dubban al’ummar Ukraine na tururuwar barin ta zuwa kasashen makwabta bayan barkewar yakin.

Kasar Hungary ta ce jerin motocin ’yan Ukraine da tsawonsu ya haura kilomita uku sun yi jerin gwano suna neman shigaowa kasarta.

Gwamnatin kasar ta harmata wa maza masu shekaru sama da 17 barin kasar, inda ta umarce su da su tsaya su kare kasarsu.

Rasha ta kwace masana’antar nukiliyar Ukraine

Dakarun Rasha da suka kutsa cikin Ukraine daga kasar Belarus sun kwace cibiyar makamashin nukiliya ta Chernobyl da ke Ukraine, bayan sun gwabza kazamin fada da sojojin Ukraine.

Kawo yanzu dai ba a bayyana adadin sojojin da fadan ya ritsa da su ba a cibiyar nukiyar, amma gwamantin Ukraine na zargin sojojin na Rasha sun tsare ma’aikatan tsaron cibiyar nukiliyan.

A cibiyar aka samu iftila’in nukiliya mafi muni a tarihin duniya, inda a shekarar 2014, inda daya daga cikin rumbunansa na nukiliya hudu ya yi bindiga, lamarin da ya haifar da damuwa a yankin Gabashin Turai.

Daga baya an gyara wajen amma, har yanzu akwai ragowar dagwalon nukiliyar da ba a kammala sharewa ba.

Ministan Tsaron Rasha, Sergiy Lavrov, ya ce kasarsa ta kwace cibiyar makamashin nukiliyar ce a matsayin kashedi ga kungiyar tsaro ta NATO cewa Rasha ba za ta raga wa duk wanda ya nemi yi mata katsalandan ba.

Shugaban Hukumar kula da nukiliya ta Ukraine, Sergiy Korsunky, ta ce yanayin zafin wajen ya karu kwarai, tana mai gargadi cewa sojojin da suka kwace shi ba su san yadda za su kula da shi ba.

Rasha na shirin kwace Kiev

Gwamnatin Ukraine takuma umarce al’ummar kasar da su nemi mafaka, ko zu zauna a cikin gidajensu a yayin da dakarun Rasha ke kokarin mamaye Kiev, babban birnin kasar.

Ukraine ta zargi sojojin Rasha dai kai hari kan gine-ginen farar hula akalla 32 a cikin sa’a 24 da suka gabata, kuma sun kasha akalla mutum 100, ciki har da kananan yara.

Magajin garin Kiev, babban birnin Ukraine ya ce wani makami mai linzami da aka harbo a cikin daren Juma’a ya kashe mutum uku a birnin.

Ma’aikatar Tsaron Ukraine ta ce dakarun Rasha na shirin yi wa birnin Kiev kawanya a ranar Juma’a, lamarin da ya tilasta wa mazauna kaurace wa gidajensu.

Ta ce sojojinta sun hallaka sojojin Rasha sama da 1,ooo — ikirarin da ba kai ga tantancewa ba.

An yi wa Rasha taron dangi

Tuni dai gwamnatoci da kungiyoyin kasashen duniya sun kakaba wa Rasha takunkumin karya tattalin arziki bayan Gwamnatin Shugaba Vladimir Putin ya kaddamar da yakin a ranar Alhamis.

Amurka ta haramta wa bankunan SBERBANK da VTB na Rasha canjin Dala, ta kuma sanya takunkumi ga wasu bankunan Rasha biyu, ciki har da wanda rundunar tsaron Rasha ke amfani da shi wajen gudanar da cinikayya.

Takunkumin bai shafi bangaren mai da iskar gas na Rasha ba, a wani mataki na kauce wa tashin farashinsu; Rasha ce kasa ta biya a duniya waje samar da danyen mai, kuma ta farko wajen samar da iskar gasa a nahiyar Turai.

Shugaba Biden na Amurka ya ce mai makon haka, kasarsa za ta fito da man da take da shi a ajiye domin daidaita farashinsa a kasuwar duniya.

Tuni da ma dai Jamus ta dakatar da yarjejeniya shimfida bututun iskar gas na NORD Stream 2 da take shirin kulla yarjejeniya da Rasha.

Kasashen Amurka da Japan da Taiwan sun dakatar da fitar da kayayyaki, ciki har da kayakin soji zuwa Rasha.

An kuma sanya takunkumi a kan wasu kamfanonin gwamnati, ’yan majalisa da jami’an gwamnatin Rasha.

Kazalika Shugaban Turkiyya, Recep Teyep Erdogan ya yi tir da matakin na Rasha Ukraine.

Birtaniya ta sanay wa kamfanin sufurin jiragen EAROFLOT na Rasha, matakin da ya sa nan take Rasha ta haramta wa jiragen Birtaniya shiga kasarta.

Sai dai China ta la’anci takunkumin da kasashen suka sanya wa kawarta Rasha, tana mai kiran takunkumcin da cewa haramtacce ne.

Ukraine na neman taimako

Shugaba Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bukaci kasanshen duniya da su kawo musu dauki.

Ya bayyana cewa akwai bukatar daukar kwararan matakan gaggawa a kan Rasha, domin sanya mata takunkumi kadai ba shi ne mafita ba.

Zelenskyy ya bayyana cewa shi ne babban wanda Rasha ke neman kaiwa a gare shi, domin kawar da shi a doron kasa.

Shugaba Kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya yi kira ga kasashen duniya ya katse hualr cinikayya da Rasha gaba daya.

Tuni gwamnatin Turkiya ta bayyana shirinta na tura tawagar ma’aikatan agaji zuwa Ukraine domin kula da majinyata.

Tarayyar Turai ta ware Dala biliyan 1.7 a matsayin tallafi da za su aike da shi ga Ukraine.

A nasa bangaren, kotun ICC ta ce za ta gudanar da bincike kan yiwuwar aikata laifukan yaki da tauye hakkin dan Adam mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.

Kasuwar Rasha ta fara girgiza

Duk da matakan da aka dauka kan Rashar, tattalin arzikinta bai girgiza ba nan take.

Rasha tana da akalla Dala bililyan 600 a asusunta, wanda ake ganin zai taimaka mata wajen tsallake radadaen takunkuman.

Sai dai rahotanni daga Moscow sun ce ’yan kasar sun shiga cikin yanayi na dar-dar, game da irin tasirin da tunkuman za su yi musu a nan gaba.

Tun a ranar Alhamis da aka fara sanya takunkumin, farashin kayan laturoni suka tashi da kasha 30 cikin 100 a Rasha.

Kazalika kasuwar hada-hadar hannun jarin kasar ta yi kasa da kasha 20 cikin 100.

Kazalika darajar kudin kasar, Rubble, ya fadi a kasuwar canjin kudi, musamman ta canjin Dala.

Gwamnatin Rasha ta tsare ’yan kasarta akalla 1,800 da suka fito zanga-zangar adawa da yakin da ta kaddamar a Ukraine.

Mutane na sayen makamai

A yankin Zaporizhzhia da ke Kiev, mutane na tururuwar zuwa sayen makamai tare da yin cefane, bayan samu labarin cewa sojojin Rasha sun doshi yankin da ke Gabashi da kuma Arewa maso Gashin Ukraine.

A cikin dare ne dai aka harba makami mai linzami a kan wani bene mai hawa takwas, inda ya kona shi.

A yankin Mariopaul mutane na fama da karancin kayan bukatun yau da kullum da kuma ruwan sha bayan sojojin Rasha na luguden wata babu kakkautawa.