✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwale-kwale ya hallaka mutum 5 a Nasarawa

A kalla mutum biyar ne suka rasu yayin da mutum uku suka bace lokacin da wani kwale-kwale ya kife a wani babban kogi da ke kauyen…

A kalla mutum biyar ne suka rasu yayin da mutum uku suka bace lokacin da wani kwale-kwale ya kife a wani babban kogi da ke kauyen Ashangwa a yankin Raya Kasa na Lafiya ta Kudu a Jihar Nasarawa a karshen mako jiya.

Wakilinmu wanda ya ziyarci inda lamarin ya auku, ya gano cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a gano wadanda suka bace a kogin bayan da kwale-kwalen ya kife da su ba.

Daya daga cikin wadanda suka tsira a hadarin mai suna Madam Felina Agwale ta alakanta faruwar lamarin ne ga yarinta da rashin kwarewar matukin kwale-kwalen, wanda a cewarta shekarunsa sun gaza ya tuka kwale-kwalen. Ta ce shi ya sa lokacin da kwale-kwalen ya fara nuna alamun kifewa a tsakiyar kogin bai iya shawo kansa ba har ya kife da su a tsakiyar kogin.

Dagacin Ashangwa, Mista Joseph Mamman Amagbo ya nuna damuwarsa dangane da aukuwar lamarin wanda ya ce ya yi ta faruwa a kai-a-kai a yankin. Ya alakanta hakan ga sakacin da wadansu fasinjojin kwale-kwalen ke yi na barin kananan yara suna tuka su a a cikin kogin.

Ya yi kira ga fasinjojin su daina yin kasada a yayin da suke shiga kwale-kwalen, su rika tantance mutanen da suka mallaki hankalinsu, sannan suka kware a tukin don kare rayuka da dukiyoyinsu.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Barista Zakari Alumaga ya tabbatar da aukuwar lamarin,  lokacin da wakilinmu ya tuntube shi. Sai dai ya ce har zuwa lokacin yana jira ne ya samu cikakken bayyani kan yadda hadarin ya auku. Ya ce hukumar ta turo wadansu jami’anta yankin cikin gaggawa don neman wadanda suka bace a kogin.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Usman Isma’ila ya bayyana wa wakilinmu ta tarho cewa rundunar ba  ta samu labarin kifewar kwale-kwale a yakin ba. Amma ya yi alkawarin za su gudanar da bincike a kan lamarin.

Binciken wakilinmu, ya gano cewa mazauna kauyen Ashangwa da kewaye suna amfani da kwale-kwale ne wajen ketare wannan babban kogi da ke tsakaninsu da sauran kauyuka da garuruwan yankin don gudanar da harkokin kasuwanci da noma da sauransu.