✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikon amana: ’Yan Najeriya 9 da suka nuna halin kwarai a duniya

A kwanakin baya Hukumar Binciken Miyagun Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta fitar da sunayen ’yan Najeriya 77 da ake zargi da aikata laifuffuka ta Intanet, al’amarin…

A kwanakin baya Hukumar Binciken Miyagun Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta fitar da sunayen ’yan Najeriya 77 da ake zargi da aikata laifuffuka ta Intanet, al’amarin da ya shafa wa kasar nan kashin kaji a idon duniya. Haka kuma ya haddasa mayar da martani daga wadansu ’yan Najeriya, wadanda suka tsaya kai da fata cewa lalacewar kasar bai kai yadda ake  kallonta ba. Hasali ma sun ce ai mutanen kasar nan mutane ne nagari masu gaskiya da rikon amana.

Aminiya ta binciko sunayen wadansu zaratan ’yan Najeriya 9 da suka nuna abin misali wajen rikon amana a duniya, inda labaransu suka ja hankalin kafofin labarai na duniya, kan yadda suka gwada nagartarsu wajen mayar da wasu makudan kudi da ko dai suka yi tuntunben tsintarsu ko kuma an tura musu a asusunsu na ajiya a banki bisa kuskure.

Wadannan ’yan Najeriya da suka nuna hali nagari abin koyi sun hada da:

 

Malam Abubakar Garba, Dan Fansho a Jihar Bauchi

Abubakar Garba, mai shekara 67 wanda ya yi ritaya a shekarar 2011, ya kasance yana ta kai-kawo cikin ragaita don neman a biya shi kudin garautinsa tun wancan lokaci. Kudin garatutinsa duka Naira miliyan 1 da dubu 239 da 777 da kwabo 45 ne, ko Naira miliyan daya da rabi da su kai ba. Sai dai ya yi sa’ar an biya shi Naira miliya daya, a matsayin rukuni na farko a bana.

Bayan wasu watanni, an sake kiransa da ya zo ya karbi sauran kudin; kwatsam sai kawai ya tarar da ilahirin kudaden garatutin nasa rubuce a cekin kudin, wato Naira miliyan  1 da dubu 239 da 777 da kwabo 45.

Sai Malama Garba ya debi iya abin da ya rage na cikon hakkinsa daga cikin kudin, kana ya dauki sauran Naira miliyan daya da aka kara masa cikin tsanaki ya mayar da su ga lalitar gwamnatin jihar.

A nemi jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.