✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Warri ya ga dal, ya koma wa gargajiya

Bayan kwanaki hudu da aka yi ana zanga-zanga kan watsin da Sarkin Warri, Olu na Warri, Ogiame Atuwase Na Biyu ya yi da sunan sarautar…

Olu na Warri, Ogiame Atuwase Na BiyuBayan kwanaki hudu da aka yi ana zanga-zanga kan watsin da Sarkin Warri, Olu na Warri, Ogiame Atuwase Na Biyu ya yi da sunan sarautar gargajiya ta Ogiame din, yanzu ganin dal ta sa ya koma mata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa sarkin na kabilar Itsekiri ya lashe amansa, ya koma wa bukatar talakawansa na lallai ya yi riko da gargajiya, a yayin da ya ga talakawan na neman kunno masa wuta.
An yi zargin cewa sarkin ya yi nufin ajiye sunan mukamin gargajiyar kuma zai canja shi da wani da ba ambata shi ba, amma mutanensa na Itsekiri suka nuna rashin amincewarsu kan haka.
Sarkin, wanda ya nuna cewa sunan mukamin yana da alaka da wata gunki ta teku, ya ce ba shi da wata alaka da gunkin.
’Yan kabilar ta Itsekiri sun fara zanga-zangar ce a ranar 7 ga wata, yayin da suka mamaye fadar Atuwasen don su nuna rashin amincewarsu da abin da sarkin yake da niyyar yi.
Wasu cikin matan Itsekiri sun yi shirin tasu zanga-zangar a ranar Talata, amma kafin ranar, sarkin ya yarda da abin da jama’arsa ke so.
Wata sanarwa da sarakuna 22 suka bayar a lokacin da zanga-zangar ta yi kamari, ta soki lamirin matakin da sarkin ya nemi ya dauka.  daya daga cikinsu, Misis Rita Lori-Ogbebor, wadda ta karantar takardar sanarwar, ta ce sunan mukamin Ogiane ba shi da wata alaka da wani gunki.  “A lardin Warri akwai Kiristoci da Musulmi da maguzawa”, inji ta.
Masu zanga-zangar sun nuna cewa sai dai sarkin ya bar kujerarsa, matukar ya ajiye sunan mukamin Ogiane, wanda ke nufin sarkin dukan allolin ruwa.Bayan da ya amince da rike mukamin ne, sai kowa ya bi, aka sake mubaya’a, aka bayyana amincewa da goyon baya.