✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya Kashe Matarsa Kan Zuwa Ganin Danta A Gidan Tsohon Mijinta

Magidancin ya caccaka wa matarsa almakashi har ta ce ga garinku nan

Wani mutum mai shekaru 40 ya aika matarsa lahira saboda za ta je ganin danta a gidan mininta na fari.

Magidancin ya caka wa matar tasa almakashi ne a yayin gardamar da ta barke a tsakaninsu bayan daukar dogon lokaci suna zaman doya da manja.

Makwabtantan ma’aratan da ke zaune a garin Akure a Jihar Ondo sun shaida wa wakilinmu cewa, sun sha yi musu sulhu amma abin ya ci tura.

Daya daga cikin makwabtan ya ce, “Abin takaici ne a ce ya kashe matarsa. Mun sha yi musu gargadi game da yawan fadan da suke yi tsakaninsu amma ba su bari ba.

“Danginsu su ma sun shiga tsakani amma duk da kokarin da aka yi wurin sasanta su zaman ya ki dadi. Da ma rabuwa suka yi kowa ya yi hanyarsa da  wannan abin bakin ciki da bai faru ba.”

Kakakin ’yan sanda a jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce, “Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin da matarsa suna yawan yin rigima kan batun zuwa duba yaronta a gidan tsohon mijinta.

“Wanda ake zargin bayan ya kashe matar, ya dauki hotunan gawar sannan ya kulle ta a gidan har cikin dare kafin ya yi kururuwar neman dauki”.

Kawo yanzu dai wanda ake zargin yana hannun hukuma ana gudanar da bincike da nufin daukar mataki na gaba.