Daily Trust Aminiya - Taho-mu-gamar motoci ta kashe mutum 15 a Borno
Subscribe

Taho-mu-gamar motoci ta kashe mutum 15 a Borno

Mutum 15 sun rasu a wata taho-mu-gama da wasu motocin bas biyu suka yi a hanar Maidugri zuwa Damaturu a ranar Jama’a.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC) Reshen Jihar Borno, Sanusi Ibrahim ya ce hatsarin ya auku ne da kauyen Mainok a Karamar Hukumar Kaga da ke jihar.

“Na samu rahoto daga ofishinmu na garin Beneshiek cewa motocin sharon guda biyu dauke da mutum 15 har da direbobinsu sun yi taho-mu-gama, mutanen duk suka rasu.

“Mutanen sun hada da maza bakwa da mata takwas,” inji Ibrahim wanda ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar taya da ya sa mota kwace wa daya daga cikin direbobin.

Ya ce an kai gawarwakin Babban Asibitin garin Benisheik, Hedikwatar Karamar Hukumar ta Kaga.

Ya yi kira ga masu ababen hawa da su rika kiyaye ka’idojin tuku domin a samu raguwar hadura.

More Stories