✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Takarata ba ta ko a mutu ko a yi rai ba ce — Kwankwaso

Ya ce ya fito ne don ya ci gaba da hidimta wa Najeriya

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce takarar shi ta neman Shugabancin Najeriya a 2023 ba ta ko a mutu ko a yi rai ba ce.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a shirin siyasa na Politics Today na gidan Talabijin din Channels ranar Litinin.

Kwankwaso wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano ne ya ce shi da masu akida irin ta sa sun shiga jam’iyyar NNPP ne domin su ceto kasar nan daga mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki.

Ya cigaba da cewa: “Mun gaji da wannan tsohon tsarin na gafara sa amma ba mu ga kaho ba, shi ya sa muka shigo jam’iyyar NNPP domin kawo sauyi.

“Yadda abubuwa ke tafiya a kasar nan komai a lalace yake, kowa hankalinsa ba a kwance yake da lamarin tsaron kasar ba, shi ma tattalin arzikin a durkushe yake. Sauran bangarorin ilimi da al’ada suma duk sun mutu,” inji Kwankwaso.

Haka zalika ya ce “Akwai bukatar a samar da hadin kai tsakanin al’ummar Arewaci da Kudancin kasar nan, saboda rarrabuwar kai ya yi yawa a kasar, don haka za mu yi kokarin hada kai mu ba wa kowanne bangare dama iri daya.

“’Yan siyasa a ra’ayina sun sangarce. Ba wai na fito takara ba ne don na fito daga yankin Arewa maso Yamma ba, a’a sai don ni dan Najeriya ne, na hidimta mata tukuru tsawon shekara 17 a matsayin ma’aikaci.

“Abin da ’yan Najeriya ke cewa shi ne suna son dan takarar da ya dara kowanne, kuma a kowanne lokaci ina mai tabbatar wa da kowa cewa ba a matse nake na yi Shugaban Kasa ba,” inji dan takarar Shugaban Kasar.