✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talban Zazzau ya riga mu Gidan Gaskiya

Talban Zazzau, Alhaji Alhaji Abdulkadir Pate ya riga mu gidan gaskiya. Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar basaraken ne ranar Juma’a 1 ga watan Janairu,…

Talban Zazzau, Alhaji Alhaji Abdulkadir Pate ya riga mu gidan gaskiya.

Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar basaraken ne ranar Juma’a 1 ga watan Janairu, 2020.

Iyan Zazzau: Karfe hudu za a yi Sallar Jana’iza a Zariya

“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Masarautar Zazzau na sanar da rasuwar Talban Zazzau, Alhaji Abdulkadir Pate.

“Allah SWT ya ba wa iyalansa juriyar wannan rashi, Ya gafarta masa kurakuransa, sannan Ya sa Aljannh Firdausi ce makomarsa. Amin,”inji sakon da masarautar ta wallafa a shafinta na Twitter.

A ranar Juma’ar ce kuma Masarautar ta sanar cewa Allah Ya yi wa Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu rasu, bayan fama da rashin lafiya.

Iyan Zazzau ya a Legas, bayan fama da zazzabi na kwana daya, yana da shekara 70 a duniya.