✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Tashar lantarki ta Kashinbila za ta fara aiki a 2022’

Majiyarmu a tashar ta ce an kammala tashar har an yi gwaji kuma komai lafiya

Tashar wutar lantarki ta Kashinbila mai karfin megawatta 40 za ta fara aiki a shekarar 2022 mai kamawa.

Binciken Aminiya ya gano cewa an kammala aikin tashar wutar lantarkin da ke Takum a Jihar Taraba, ana kuma shirin kaddamar ta ita a farkon 2022.

Majiyarmu a tashar ta Kashinbila da ta nemi a sakaya sunanta ta ce an riga an kammala tashar ta Kashinbila, har an yi gwaji kuma komai lafiya lau.

Majiyar ta ce abin da ya rage shi ne hada line lantarki mai karfin 33kv na yankin Kudancin Jihar Taraba.

A halin yanzu bututan samar da wuta guda hudu da ke tashar — wadanda kowannensu ke da karfin megawatta 10 — suna aiki 100 bisa 100.

Layin tura wutar lantarkin mai karfin 132Kv kuma an hada shi da karamar tashar da ke Yandev a Jihar Binuwai, domin samar da wutar a jihohin Filato, Bauci da Gombe.

Kananan hukumomin Takum, Ussa, Donga, Wukari da Ibbi na Jihar Taraba kuma za a hada su da tasha mai karfin 33KV.

Bincikenmu ya gano cewa za a fara tura wuta daga sabuwar tashar ce da zarar komai ya kammala, kuma za a hada shi da matattara wutar lantarki ta kasa wadda ba a hada da yankin Taraba ta Tsakiya ba.

Kananan hukumomin da ke yankin — Sardauna, Gassol, Bali da Gashaka na Jihar Taraba — na fama da kuma babu alamun za su amfani da tashar ta Kashinbila.