✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taskun da Karancin Dala a Bankuna ya jefa Dalibai da Masu neman magani a Kasashen Waje

Wan binciken da Aminiya ta gudanar  ya gano yadda ’yan Najeriya masu bulaguro ke shan wahala wajen samun Dalar a farashin Babban Bankin Najeriya (CBN).…

Wan binciken da Aminiya ta gudanar  ya gano yadda ’yan Najeriya masu bulaguro ke shan wahala wajen samun Dalar a farashin Babban Bankin Najeriya (CBN).

Wannan lamari dai ya haifar da tsaiko ga samun kudin guzurin tafiyar ’yan kasuwa (BTA), da na sauran matafiya (PTA) , ciki har da masu neman magani a kasashen waje da sauran su.

Wani mai suna Abdullahi Ahmad da ya kammala shirye-shiryen bulaguro zuwa Dubai domin duba lafiyarsa ya ce sati biyu ke nan da cike takaradar neman canjin Dala 4,000 a banki amma ta gagara samuwa.

“Sati biyu kawai ya rage min bizata ta tashi daga aiki kuma har yanzu ban samu canjin Dalar ba.

“Da dan uwana ya tuntubi manajan bankin cewa ya yi sai dai idan za mu ba da Naira 340,000 kafin mu samu a karshen satin nan; duk da na bayar ina fargabar sai na sake biza”.

Wani dan canji a kasuwar bayan fage a Kano ya ce bankuna ne suka durkusar musu da hanyar neman abincinsu, domin sun sa Dalar ta yi karancin a hannun mutane kuma ta yi tsada.

Ya ce yaznu bankunan na bada Dalar ce kawai ga wadanda suka bada kudi mai yawa, shi ya sa kullum take kara tsada.

A shafukan sada zumunta ma, musamman Twitter, daliban Najeriyar da ke karatu a kasashen waje sun bayyana halin da suke ciki da bankunan idan sun je karbar kudaden guzurinsu.

Wata mai suna Mavis Ikpeme ta koka kan yadda bankunan suka sanya sharudda masu tsauri kafin samun Dalar, wanda ya tilasta mutane komawa saye ta bayan fage.

Ta ce, “Ba za ka iya karbar PTA ko BTA ba ta bankuna yanzu; Matafiya ba su da mafita sai dai su je wurin masu canji na bayan fage. Shin Babban Banki ba shi da labarin abin da bankunan ke yi ne?”.

Wani mai suna Olayinka Biu, cewa yayai da gangan bankunan ke yi wa masu neman Dala haka, domin a cewar sa suna bayar da ita ga kamfanonin canjin kudi.

“Babbar matsalar ita ce masu neman PTA yanzu ba sa samu a bankunan. Suna fakewa da Dala ta yi karanci da kuma dogayen layi a matsayin abin da ya sanya mutane ba sa samun ta a kan lokacin har lokacin tafiyarka ya yi.

“Kuma bayan ga masu kasuwannin bayan fage nan na samu cikin sauki a wurinsu”, in ji Olayinka.

Abin da bankuna ke cewa

Wani Babban jami’in banki a Legas ya sanar da wakilinmu cewa tushen matsalar shi ne karacin Dalar a kasuwar musayar kudi.

“Da gaske ne muna fama da karancin Dala a hannunmu amma muna iya bakin kokarinmu don share wa masu neman ta a hannunmu hawaye.

“A yanzu dai muna kokarin bai wa wadanda suka fi bukatar ta ne fififko.

“Wani abin da ke kara haddasa matsalar shi ne masu rubuto takardun bulaguro ta jabu kawai don su samu Dalar.”

Abin da bankin CBN ke cewa

Daraktan Sashen Sadarwa na Babban Bankin Najeriya (CBN), Osita Nwanisobi ya ce suna daukar matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar.

Ya ce duk da akwai bukatar duba bukatar marasa lafiya da ’yan kasuwa da dalibai masu biyan kudin makaranta a kasashen waje, CBN na duba halin da farashin Naira zai kasance a kasuwar canji ta duniya.

Ya kuma ce Bankin na tanadin dabarun taimaka wa Najeriya samun karin kudin shiga mai dorewa duba da yadda kudin da take samu ta bangaren danyen man fetur ke kara faduwa kullum.

Daga: Rahima Shehu Dokaji, Abiodun Alade (Legas) & Zahraddeen Y. Shuaibu (Kano)