Tinubu: Bayani kan dan takarar shugaban kasar APC a 2023 | Aminiya

Tinubu: Bayani kan dan takarar shugaban kasar APC a 2023

    Bashir Isah

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Adekunle Tinubu, an haife shi ne a ranar 29 ga Maris, 1952.

Fitacce dan siyasar mai fada a ji a shiyyar Kudu maso Yammacin Najerya, shi ne tsohon gwamnan Jihar Legas, kuma masani ne kan hada-hadar kudi.

Tinubu ya yi karatunsa ne a Kasar Amurka, kuma ya yi aiki na wasu shekaru a kasar waje kafin dawowa gida Najeriya a shekarun 1980, inda ya ci gaba da aiki sannan daga bisani ya shiga harkar siyasa.

Ya zama Sanata mai wakiltar Mazabar Legas ta Yamma a Majalisar Dattawa a shekarar 1992 karkashin Jam’iyyar SDP.

Duk da matsin lamba ya tilasta wa Tinubu gudun hijira a 1994, daga bisani ya dawo gida bayan rasuwar Marigayi Shugaba Abacha a 1998 inda Jamhuriya ta Hudu ta kankama.

Bayan da Marigayi Sani Abacha ya rushe ‘Yan Majalisar Dattawa a 1993, Tinubu ya zama dan gwagwarmaya mai rajin dawo da tsarin mulkin dimokuradiyya.

Ya mulki Jihar Legas a matsayin gwamna na wa’adi biyu (shekara takwas), kuma a karkashin Jami’iyyar AD daga 1999 zuwa 2007.

Bayan nan, Tinubu ya ci gaba da zama fitaccen dan siyasa mai tasiri a Najeriya, wanda hakan ya ba shi damar taka muhimmiyar rawa wajen kafa jami’iyyar APC a 2013 inda ake ta damawa da shi har zuwa wannan lokaci.

A watan Janairun 2022 ne dan siyasar ya bayyana aniyarsa ta zawarcin shugabancin Najeriya a shekarar 2023.

A matsayinsa na daya daga cikin ’yan takarar Shugaban Kasa, Tinubu ya nuna wa jam’iyyarsa ta APC cewa yanzu lokaci ne da ya kamata a ba shi dama ya mulki Najeriya, musamman ma idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da bai wa jam’iyyar wajen lashe manyan zabubbukan da suka gabata.