✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya gabatar da Kasafin Kudin 2024

Shugaban zai tafi Dubai a ranar Alhamis domin halartar taron sauyin yanayi.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2024 ga zaman Majalisar Dokokin kasar nan a ranar Laraba cikin minti 25 kacal.

Shugaban ya fara gabatar da kasafin kudin ne da misalin karfe 11:40 na safe kuma ya kammala da misalin karfe 12:05.

Yawanci shugabannin baya kan dauki lokaci mai tsawo suna gabatar da kasafin kudinsu ga majalisar dokokin kasar nan.

Ana sa ran shugaban zai tafi Dubai domin halartar wani taro a ranar Alhamis.

 

Bayani na tafe…