✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya janye kalamansa kan daukar matasa miliyan 50 aikin soja

Jagoran na APC ya yi karin haske kan kalaman nasa.

Jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce subul da baka ya yi game da kiran da ya yi wa Gwamnatin Tarayya na daukar matasa miliyan 50 aikin soji. 

Mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce tsohon gwamnan na Jihar Legas na nufin gwamnati ta dauki matasa dubu biyar aiki, don magance matsalar tsaro.

A ranar Litinin ne Tinubu ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Buhari da ta dauki matasa miliyan 50 aikin soji don magance ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Wannan kira na Tinubu na zuwa ne lokacin da yake jawabi yayin bikin ranar zagayowar haihuwarsa wanda aka gudanar a fadar Gwamnatin Kano.

Sai dai kalaman Tinubu sun bar baya da kura, inda wasu daga ciki da wajen jam’iyyar APC ke suka tare da mayar da martani.

Kazalika, Tunde Rahman ya nuna cewa kalaman da jagoran jam’iyyar ya yi an yi musu mummunar fahimta.