✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya sauke shugaban hukumar tattara haraji, ya nada sabo

Tinubu ya tura Nami hutun wata uku gabanin ritayarsa a watan Disamba

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada Zacch Adedeji a matsayin sabon Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS), inda ya sauke mai ci, Mohammed Nami.

Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelele ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da yammacin Alhamis.

Ya ce tuni Tinubu ya umarci Nami ya tafi hutun ajiye aiki na tsawon wata uku, kamar yadda dokar aikin gwamnati ta tanada a shirye-shiryen yin ritayarsa ranar 8 ga watan Disamba mai zuwa.

Ngelale ya ce bisa ga umarnin na Shugaban Kasa, nadin ya fara aiki nan take.

“Hon. Zacch Adedeji zai karbi ragamar shugabancin hukumar na tsawon kwana 90 a matsayin rikon-kwarya, kafin daga bisani a tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Kasa (FIRS), na tsawon shekaru hudu.

“Hon. Zacch Adedeji Akanta ne da ya yi karatu a Jami’ar Obafemi Awolowo, inda ya kammala da digiri mai daraja ta daya. Ba da jimawa ba ya rike muƙamin mai ba shugaban kasa shawara kan tattara haraji, bayan ya yi Kwamishinan Kudi a Jihar Oyo,” in ji sanarwar.