✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump ya sake ikirarin magudin zabe

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ikirarain an yi masa magudi ba tare da ya bayar da wata hujja ba a shafinsa na Twitter. Ya…

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ikirarain an yi masa magudi ba tare da ya bayar da wata hujja ba a shafinsa na Twitter.

Ya yi zargin an yi aringizo a kidayar kuri’un da aka kada, sai dai bai iya ba da wani dalili kan hakan ba.

A shafinsa na Facebook kuma, Trump ya yi ta ikirarin cewa ‘Za mu ci zaben…’.

Ana dai ci gaba da kidayar kuri’u a jihohin Amurkar ciki har da Arizona da Georgia, sai dai har yanzu, dan takarar jam’iyyar Democrat, Joe Biden ne ke kan gaba.

Masu sharhin siyasar kasar na cewa da wuya matakan kalubalantar zaben gaban kotu ko kuma kidayar su iya sauya nasarar ta Biden.

Duk da ikirarin Trump, masu sa ido na kasashen duniya daga Kungiyar Jihohin Amurka, OAS, sun yaba da yadda aka gudanar da zaben.

Ayarin wanda ya kunshi kwararru 28 da masu sa ido daga kasashe 13 ya bayyana amincewarsa da yadda aka gudanar zaben gaba daya.

Masu sa idon sun ce sun samu damar bibiyar zaben tun daga gangamin yakin neman zabe har zuwa kada kuri’ar da aka yi ranar 3 ga watan Nuwamba a yankunan kasar da dama ciki har da jihohin da fafatawar ta yi zafi wato Georgia da Michigan.

Sun ce ba su samu shaida cewa an aikata wani magudi ba, yayin da suke martani game da ikirarin Mista Trump cewa ’yan jam’iyyar Democrat sun yi aringizon kuri’u.