✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsadar kayayyaki ta karu a Najeriya —NBS

Tun daga 2016 zuwa yanzu farashin kayayyaki sun ci gaba da ninkuwa a Najeriya.

An ci gaba da samun hauhawa na farashin kayayyaki a Najeriya kamar yadda Hukumar Kididdiga ta kasar ta bayyana a ranar Litinin.

Rahoton na hukumar NBS ya ce an samu hauhauwar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi da ya kai kashi 16.82 cikin dari a watan Afrilu da ya wuce.

An samu hauhawar farashin kayayyakin a watanni uku a jere a bana kadai.

Alkaluman NBS sun nuna tsadar kayayyakin ta ci gaba da lunkawa a Najeriya tun 2016 kawo yanzu.

Tsadar man dizel da mafi yawanci ƴan Najeriya ke dogaro da shi wurin kasuwanci ya kara haifar da tsadar kayayyakin da kuma tasirin rikicin Ukraine.