✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar rayuwa ta sa magidanta satar abinci a gonaki a Taraba

Masu gonaki sun koka kan ƙaruwar magidanta da ake kamawa rana tsaka sun saci rogo ko doya ko masara a gonakin wasu da nufin ciyar…

Rahotanni sun nuna an samu yawaitar magidanta da ke zuwa satar amfanin gona domin ciyar da iyalansu, a sakamakon tashin gwauron zabin kayan masarufi da kuma matsin rayuwa a Jihar Taraba.

Masu gonaki a wasu ƙauyukan jihar sun koka game ƙaruwar magidanta da ake kamawa da rana tsaka sun saci rogo ko doya ko masara a gonakin wasu da nufin ciyar da nasu iyalan.

Wata mai gonar rogo a Karama Hukumar Ardo-Kola, Lami John, ta shaida wa wakilinmu cewa ta sha kama maƙwabtanta sun saci rogo a gonarta.

Malama Lami ta ce mutum na farko maƙwabcinta ne kuma mutumin kirki ne, inda ya shaida mata cewa ya shiga gonarta ya ɗebi rogon ne domin kai wa iyalansa su ci, amma ba don ya sayar ba.

“Sai na ce masa ya tafi, kuma ban kai ƙara wurin mai gari ba saboda a iya sanina da shi mutum ne mai rikon amana,” in ji ta.

Lami ta ce daga baya an samu ƙaruwar maƙwabtanta magidanta da ke shiga gonar tata su saci rogo domin su ciyar da iyalansu.

Saboda haka ta yi sauri ta girbe gonar amma ta bar wani ɓangare saboda maƙwabtanta da ba su yi noma ba su samu abin da za su ɗiba.

Binciken wakilinmu ya kuma gano cewa satar doya da masara a gonaki ma ta zama ruwan dare a ƙauyuka da dama a sasan jihar.

Wani manomi mai suna Ibrahim Suleiman, ya shaida masa cewa sau huɗu yana kama wasu makwabtansa da suka shiga gonarsa suka saci masara.

Amma ya ce bai kai ƙara wajen ’yan sanda ko mai gari ba, saboda maƙwabtan nasa ba a taɓa samun su da aikata ayyukan laifi ba.

Don haka ya ce yana kyautata zaton matsin rayuwa ne ya sa su yin hakan.

Manomin ya ƙara da cewa yanzu da rana tsaka mutane ke zuwa su saci amfanin gonakin wasu, kuma waɗanda aka kama daga cikinsu sukan amsa da cewa talauci da rashin abinci ne suka sa su satar amfani gonakin wasu.