✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsawa ta fada wa karamin yaro

Karamin yaro ya rasu bayan tsawa ta fada masa a wurin wasan kwallon kafa.

Wani karamin yaro ya rasu bayan da tsawa ta fada masa a yayin da ake ruwan sama da iska mai karfi.

Tsawar ta fada wa yaron wanda yake aji 1 na Karamar Sakandare ne a yayin da ake buga wasan kwallon kafa.

Ana cikin haka ne sai kwallon ya fita daga fili, shi kuma ya je ya dauko ta, a nan ne tsawar ta fada masa, ta kashe shi.

Lamarin ya faru ne a unguwar Imiringi da ke Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa, ranar Alhamis.

Aminiya ta tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, SP Asimin Butswat, amma ya ce ba su da labari.