✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Gwamnan Jigawa Ibrahim Aliyu ya rasu

Tsohon gwamnan ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya a Jihar Kaduna.

Allah Ya yi tsohon Gwamnan Jihar Jigawa a lokacin mulkin soji, Birgediya Ibrahim Aliyu rasuwa a ranar Juma’a.

Sanarwar rasuwar ta fito me daga hadimin Gwamnan Jigawa kan kafofin watsa labarai, Habibu Nuhu Kila a ranar Asabar.

  1. Masu fasa-kwaurin shinkafa sun bude wa kwastam wuta
  2. An fara shirye-shiryen Aikin Hajjin bana a yanayin COVID-19

Gwamnan Jihar, Muhammad Badaru ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan tsohon Gwamnan Birigediya Ibrahim Aliyu, tare da yi masa addu’ar samun rahama.

Janar Ibrahim Aliyu wanda ya rasu a Kaduna ya shugabanci Jihar Jigawa ne daga 1993 zuwa 1996.

A baya-bayan nan Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya kaddamar da ayyukan wasu tituna a Jihar Jigawa da aka sanya wa sunan marigayin.