✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Ministan Ilimi Farfesa Agada ya rasu

Farfesa Jerry Agada ya rasu yana da shekara 68

Tsohon Minista a Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya, Farfesa Jerry Agada ya riga mu gidan gaskiya.

Da safiyar Talata Farfesa Agada ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiyar da kwantar da shi na mako guda a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Makurdi, Jihar Binuwai.

Makusantan iyalan tsohon Ministan Ilimin sun tabbatar da rasuwar a zantawarsu da wakilinmu ta waya.

Mamacin ya bar duniya ne yana da shekara sittin da takwas.

Kafin rasuwar Farfesa Agada, shi ne Shugaban Hukumar Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar Binuwai.

Shi ne kuma tsohon Shugaban Kungiyar Mawallafa ta Najeriya (ANA).