✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Shugaban Hukumar NCAA Mukhtar Usman ya rasu

Tsohon Darakta Janar na Hukumar NCAA mai Kula da Zirga-Zirga Jiragen Saman Kasar, Kyaftin Mukhtar Usman ya riga mu gidan gaskiya. Marigayin ya rasu ne…

Tsohon Darakta Janar na Hukumar NCAA mai Kula da Zirga-Zirga Jiragen Saman Kasar, Kyaftin Mukhtar Usman ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne ranar Talata bayan ya shafe shekaru 63 a a duniya.

Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jigilar Jiragen Sama, Illitrus Ahmadu ne ya tabbatar wa da ‘yan jarida rasuwar marigayin da safiyar Laraba a wata tattauna wa da ya yi da manema labarai ta wayar tarho.

Rahotonni sun ce marigayi Muhtar ya rasu ne a daren ranar Talata a wani asibiti a garin Zariya na jihar Kaduna bayan ya yi fama da gajeriyar jinya.

A watan Oktoban 2014 ne aka nada shi a matsayin Darakta Janar na Hukumar NCAA inda ya jagorance ta na tsawon shekaru biyar.

Ya kuma mika wa Kyaftin Musa Nuhu ragamar jagorancin Hukumar a watan Oktoban 2019.

Kazalika, ya taba rike mukamin Kwamishina a Hukumar Binciken Hatsarin Jiragen Sama ta Kasa.