✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Shugaban Mali, Amadou Toure ya rasu

Tsohon shugaban Kasar Mali Amadou Toumani Toure ya rasu ranar a kasar Turkiyya yana da shekaru 72. Iyalai da likitocin mamacin wadanda suka sanar da…

Tsohon shugaban Kasar Mali Amadou Toumani Toure ya rasu ranar a kasar Turkiyya yana da shekaru 72.

Iyalai da likitocin mamacin wadanda suka sanar da rasuwar tsohon shugaban sun ce ya rsau ne ranar Talata.

Dan uwan tsohon shugaban, Oumar Toure ne ya bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Marigayi Amadou wanda ya jagoronci gina kasar na shekara goma kafin daga bisani a yi masa juyin mulki, ya rasu a kasar ta Turkiyya bayan ya je domin neman lafiya.

An dai kai tsohon shugaban kasar ne kasar Turkey don yin jinya ne inda daga bisani kuma rai ya yi halinsa a can.