✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohuwar Ministar Mata Jummai Alhassan ta rasu

Tsohuwar Ministar Mata, Aisha-Jummai Alhassan, wato Maman Taraba ta rasu.

Allah Ya yi wa tsohuwar Ministar Mata, Amina-Jummai Alhassan, wadda aka fi sani da Mama Taraba rasuwa.

Bayanan sun ce Jummai Alhassan ta rasu ne a wani asibiti a birnin Alkahira na kasar Masar tana da kimanin shekara 62 a duniya.

Wani tsohon mai magana da yawun Maman Taraba, Suleiman Dantsoho, ya ce Allah Ya yi mata cikawa ne a ranar Juma’a.

Mama Taraba fitacciyar ’yar siyasa ce a Jihar Taraba, inda a shekarar 2015  ta yi takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC.

Shugaba Buhari ya nada Mama Taraba Ministar Harkokin mata, bayan Gwamna mai ci Dariusa Ishaku ya kayar da ita a zaben.

Daga baya a 2018 ta sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP, bayan jam’iyyar APC ta hana ta tsanayawa takara a zaben 2019.