✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tuban ’yan Boko Haram na jefa Borno cikin tsaka mai wuya – Zulum

Ya ce mafi yawan mutane na cikin tsaka mai wuya kan amincewa da su.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce tuba da kuma mika wuyan da mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ke yi a ’yan kwanakin nan na jefa Jihar cikin tsaka mai wuya.

A ranar Asabar ne dai Gwamnan ya kai ziyara garuruwan Bama da Gwoza, inda ya zanta da dakarun sojoji da kuma shugabannin al’umma a yankunan.

Rahotanni sun ce mafiya yawan mutanen da ayyukan ta’addanci ya shafa a Jihar na fuskantar kalubalen ko dai su karbi tubabbun ’yan ta’addan ko kuma su ki amincewa da su.

Sai dai a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Isa Gusau ya fitar ranar Lahadi, Gwamna Zulum ya ce lamarin na bukatar jin ra’ayoyi daban-daban daga dukkan masu ruwa da tsaki a yankunan sannan a duba amfani da kuma illolin karba ko kin karbar mutanen.

“Mu a Jihar Borno, muna cikin tsaka mai wuya kan ci gaba da mika wuyan da tubabbun ’yan Boko Haram ke yi. Dole sai mun duba dukkan zabukan da ke gabanmu kafin mu yanke hukunci.

“Dole mu zabi ko dai mu ci gaba da yaki har illa masha Allahu, ko kuma mu karbi tubabbun mayakan, wanda kuma cike yake da takaici ga dukkan wanda a rasa da uwansa, hatta ma ga su sojojin da aka kashe wa abokan aiki.

“Babu wanda zai ji dadi ya karbi wanda ya kashe masa iyaye, ’ya’ya ko ’yan uwa. A shekara 12 da suka gabata, mun yi ta fafata wannan yakin, mun rasa dubban rayuka,” inji Zulum.

A ’yan kwanakin nan dai sojojin Najeriya sun ce daruruwan mayakan kungiyoyin ta’addancin na ci gaba da mika wuya tare da ajiya makamansu a yankin Arewa maso Gabas.