✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turawa sun fi Larabawa taimaka wa Jihar Borno —Zulum

Duk da kusancin Larabawa da Borno, ba su damu su taimaka ba

Gwamna Babagana Zulum, ya ce kasashen Turawa sun taimaka wa Jiharsa ta Borno fiye da kasashen Larabawa, a yayin da jihar ke fama da matsalar Boko Haram 

Zulum ya ce duk da cewa al’ummar Borno sun fi kusanci da Larabawa ta fuskar addini da al’adu, amma sun fi samun taimako daga kasashen Yammacin duniya fiye da Larabawa masu tarin arziki.

Yayin karbar bakuncin Jakadan Falasdinu a Najeriya, Saleh Fheied Saleh a Maiduguri, Zulum ya yaba wa Gwamnatin Falasdinu a matsayin daya daga cikin al’ummomin Larabawa na gaba-gaba wajen taimakon jiharsa.

“Ni mutum ne mai tsage gaskiyar abin da ke a zahiri. A tsawon shekarun da muke fama da mtsaloli Amurka, Birtaniya, Japan, Canada, da sauran kasashen Turai sun nuna mana kulawa sun kuma tallafa wa mutanenmu da ke cikin mawuyacin hali da kayan abinci, magunguna da muhalli.

“Sai dai ba mu samu makamanciyar kulawar ba daga kasashen Larabawa, wadanda miliyoyin ’yan Jihar Borno ke tarayya da su a bangaren al’ada da addini, domin a Borno akwai Larabawan Shuwa.

Jakadan Falasdinu a Najeriya, Saleh Fheied Saleh a lokacin da ya ziyarci Zulum

“Mun sha tuntubar kasashen Larabawa ta hanyar ziyara da tura musu wasiku, musamman mawadata a cikinsu wadandan ba sa fama da rikice-rikice, amma yawancinsa ba su nuna damuwa ba, balantana su tallafa.

“Larabawa ba su nuna sun damu da mu ba; amma ziyararka ta dawo mana da fatar da muke da ita a gare ku, muna kuma matukar godiya,” inji Zulum ga Saleh.

Tun da farko, Jakandan na Falasdinun, ya bayyana shirin gwamnatinsa ta taimaka wa Gwamnatin Jihar Borno a bangarorin da take bukata.

“Akwai kamfanonin Falasdinawa da yawa a Najeriya, a shirye suke su hada kai da Gwamnatin Borno, mu ma a shirye muke mu yi aiki tare, mu taimaka muku da abin da kuke bukata daga gare mu,” inji shi.

Saleh ya kara da cewa ’yan Najeriya da dama mazauna Falasdinu na bayar da gagarumar gudunmuwa, cikinsu har da Fatima Barnawi, ’yar asalin Jihar Borno, wadda ta rike mukamin minista kuma Shugabar ’yan Sanda