✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turji: Dan bindiga ya sako mutum 150 a Zamfara

Turji ya sako mutane da dabbobin da ya kame bayan an tsare mahaifinsa.

Shugaban ’yan bindiga da ya jagoranci garkuwa da mutum sama da 150 a kauyukan Jihar Zamfara ya sako mutanen.

Turji wanda ya yi ta bin kauyuka yana yin awon gaba da mazauna da matafiya da dabbobi ya ce ya yi hakan ne domin jami’an tsaro su saki mahaifinsa da ke tsare a hannunsu, kuma ba zai saki kowa ba sai an sako mahaifin nasa ya yi Babbar Sallah tare da iyalansa.

“Ya sako mutanen ba tare da wani sharadi ba ne bayan masu sasanci da ke taimaka wa gwamnati tattaunawa da manyan ’yan bindiga sun sanya baki,” inji wata majiyar tsaro da ke da kusanci da lamarin.

Majiyarmu ta ce masu shiga tsakani sun taimaka an mika wa Turji mahaifin nasa a ranar Lahadi inda ya amince ya sako mutanen da ya yi garkuwa da su.

A wani murya da aka nada da wakilinmu ya samu, an ji Turji yana alkawarin sakin dukkannin mutane da dabbobin da yaransa suka sace idan har aka ba shi mahaifinsa.

“Su ba ni mahaifina. Idan har kuka kawo shi Bayan Ruwa, na tabbatar muku cewa za a saki duk wani mutum ko dabba da ke hannunmu”, kamar yadda ya tabbatar wa wani babban basarake a Karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara.

A ranar Asabar mun kawo rahoton yadda Turji da yaransa suka shiga  kauyukan Kware da Kurya da Badarawa da Keta da kuma Maberaya  suna sace mutane da dabbobi bayan kame mahaifinsa da jami’an tsaro suka yi mako biyu da suka gabata a Kazaure, Jihar Jigawa.

Rahotanni sun ce mahaifin dan ta’addan ya koma Jihar Jigawa da zama ne bayan kokarinsa na ganin dan nasa ya bar ayyukan ta’addanci ya gagara.

Jami’an tsaro sun kama dattijon ne bayan masu bayar da ke adawa da Turji sun zargi mahaifin da yi wa dan nasa dillancin shanun sata.