✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ummita: Majalisa ta bukaci a binciki zargin kisan da dan China ya yi a Kano

Majalisar ta nuna damuwa kan yadda 'yan sanda suka yi shiru a kan lamarin

Majalisar Wakilai ta bukaci Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya ya binciki zargin da ake yi wa dan kasar Chinan nan, Geng Quanrong, na kashe budurwarsa, Ummulkulthum Buhari, wacce aka fi sani da Ummita, a jihar Kano.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudurin da dan majalisar mai wakiltar mazabar Rano/Kibiya/Bunkure daga jihar Kano, Kabiru Alhasan Rurum ya gabatar a gaban majalisar ranar Laraba.

Da yake gabatar da kudurin, Rurum ya ce an aikata kisan ne a gidan su marigayiyar da ke unguwar Janbulo a birnin Kano a karshen makon da ya gabata.

Dan majalisar ya ce wacce aka kashe din ta gamu da ajalinta ne a daidai lokacin da take yi wa kasa hidima (NYSC) a jihar Sakkwato.

Ya ce, “Yadda dan Chinan ya shafe sama da awa daya yana kokarin shiga dakin Ummita da yadda ya kashe ta daga bisani ya nuna karara cewa dama ya shirya yin hakan.

“Mun damu matuka kasancewa kwana biyar bayan aikata laifin, har yanzu ’yan sanda sun ki su fito da cikakkun bayanan bincikensu a kan kisan.

“La’akari da cewa kare rayuka da mutuncin ’yan kasa shi ne babban aikin gwamnati, ya sa ya zama wajibi mu dauki wannan batun da muhimmanci, saboda iyalan marigayiyar da ma sauran ’yan jihar Kano da ma na Najeriya baki daya na son a yi aiki da doka,” inji Rurum.

Shi ma da yake tsokaci a kan kudurin, dan majalisa, Nkem Abonta na PDP daga jihar Abiya, ya ce akwai bukatar ma a duba halascin zaman Geng da kuma harkokinsa a Najeriya.

Ya ce bai kamata a kyale binciken a hannun ’yan sanda kadai ba, inda ya nemi majalisar ta sanya kwamitocinta da suka dace don su zo mata da cikakken rahoto a kai.

Nkem ya ce kisa, azabtarwa ko wulakanta dan Najeriya daga kowanne dan kasar waje ba abu ba ne da za a lamunta.

A nan ne Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila ya ba da umarnin yin shiru na minta daya domin tunawa da Ummita. (NAN)