✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsayar da ranar ci gaba da sauraron shari’ar dan China da Ummita

Dan China dai ya ce ya kashe wa marigayiya Ummita sama da N60m a lokacin da suke sharbar romon soyayya.

An tsayar da ranar da za a ci gaba da sauraren karar dan kasar Chinan nan Mista Frank Geng Quarong da ake zargi da kashe budurwarsa Ummulkusum Sani wadda aka fi sani da Ummita a Jihar Kano.

Babbar kotun jihar karkashin jagorancin mai shari’a Aminu Ado Maaji ta sanya ranar 6 ga watan Disamba domin ci gaba da sauraren karar.

A bara ce aka soma gurfanar da Mista Geng a gaban kotun da ke zamanta a Miller Road, inda ake tuhumarsa da zargin da laifin kisan kai wanda ya saba wa sashe na 221 na dokar penal code.

Kakakin babbar kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya ce an dakatar da shari’ar ce na tsawon watanni takwas saboda alkalin da ke jibintar shari’ar na cikin kwamitin alkalan da ke jagorantar shari’ar kotun sauraron kararrakin zaben da aka gudana a bana.

Ana iya tuna cewa, Mista Frank Geng Quarong, wanda ya gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kano kan zargin kisan masoyiyarsa, Ummukulsum Sani Buhari, ya tabbatar da kashe ta da wuka.

While being cross examined, the defendant told the prosecution counsel, Barrister Aisha Mahmud, that he came to Nigeria in 2019. He said he was working with BBY Textile Company and that he earned N1.5m monthly.

Yayin da ake tuhumar wanda ake zargin ya shaida wa lauyan masu kara, Barista Aisha Mahmud cewa ya zo Najeriya ne a shekarar 2019, kuma yana aiki da Kamfanin Tufafi na BBY inda yake karbar albashin Naira miliyan 1.5 duk wata.

Mista Quarong ya shaida wa kotun cewa ya kashe wa marigayiya Ummita sama da N60m a lokacin da suke sharbar romon soyayya.

Aminiya ta ruwaito, rahoton kisan Ummita ya bulla ne tun a bara, inda ake zargin a ranar 17 ga watan Satumbar baran ce Mista Quarong ya kashe masoyiyarsa a gidansu da Unguwar Janbullo daura da unguwar Kuntau da ke yankin Dorayi a Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano.