✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wayar salula ta kashe aure 3,088 a Nijar

Akwai kuma uwa uba “wayar salula”, wadda ke haifar da tashin hankali ga magidanta.

Rikici tsakanin ma’aurata da wayar salula ta haddasa ya sa an samu mace-macen aure guda 3,088 a birnin Yamai na Jamhuriyyar Nijar a shekarar 2021 da ta yi bankwana a makon jiya.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da bayyana damuwa kan karuwar mutuwar aure a kasar kamar yadda BBC ya ruwaito.

Cibiyar Bunkasa Harkokin Addinin Musulunci a Nijar ta ce yawan mutuwar auren da aka gani bara a babban birnin kasar, wani babban abu ne da ke tayar da hankali.

Wasu magidanta a Yamai sun dora alhakin wannan matsala da rashin fahimta tsakanin ma’aurata da kuma wayar salula.

Ustaz Maha mamba ne a kungiyar addinin Musulunci ta kasa ya ce “ba mu taba ganin mutuwar aure ba a Yamai kamar wanda aka samu a 2021,” inji shi.

“A baya akan samu 800 zuwa 900 a wasu lokacinmu 700, saboda ana yi ana sasanci tsakani.”

Malamin ya ce wannan kuma na iya kungiyar addinin musulunci ta kasa ne kawai, ban da wanda aka rabu ba wanda ya sani banda wanda aka je kotu da sauransu.

Karya daga bangaren maza da kuma son abin duniya daga bangaren mata suna daga cikin abubuwan da Ustaz Maha ya lissafa a matsayin dalilan da ke kashe aure.

Akwai kuma uwa uba “wayar salula”, wadda ke haifar da tashin hankali ga magidanta.