✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dirka wa ’yar shekara 13 da suke haya a gidansa ciki a Kano

Ana zargin wani magidanci a Kano da yi wa ’yar wata mata da ke zaune a gidansa ciki

Ana zargin wani magidanci a Kano da dirka wa wata ’yar shekara 13, wadda mahaifiyarta ke zaune a gidansa ciki.

A wata tattaunawarta da gidan rediyan Freedom, yarinyar ta ce tun da farko mutumin ya yi mata barazanar yanka ta da kuma tashin su daga gidansa ko su biya shi kudin haya, matukar ta fada wa mahaifiyarta cewa yana lalata da ita.

Yarinyar ta ce yanzu haka sun je asibiti saboda cikinta ya tsufa, amma likitoci sun ce ba za ta iya haihuwa da kanta ba, sai an yi mata aiki, don haka sai sun kawo jinin da za a kara mata da sauran kayayyaki, su kuma ba su da halin yin hakan.

Ta ce mai gidan nasu yana zuwa wurinta ne idan mahaifiyarta ba ta nan, “Sai ya ce idan na fada mata zai yanka ni ko ya tashe mu daga haya.

“Dama kuma ba kudin yake karba ba, saboda da bakinsa ya ce ya ba mu kyauta, tsoron haka ya sa ban fada mata ba ni kuma.

“Ba zan iya tuna ranar da ya fara kwantawa da ni ba, amma dai tun kafin ranar Arfar Babbar Sallah ne,” in ji ta.

Dangane da koya na da mata a lokacin, yarinyar ta ce babu tabbas, saboda iya masu sayar da fura ta ga suna shiga gidan nasa.

Ta kuma ce ba shi kadai ne ya taba amfani d aita ba, domin akwai wani da har waya ya saya mata, bayan ta ba shi kanta, sai dai ya tsere.

“Ba shi kadai ba ne akwai wani da ya saya min waya karama aka kwace da na je kai caji.  Amma cikin ba nasa ba ne na wanda muke haya a gidansa ne,” in ji ta.

Haka kuma ta nemi taimakon al’umma musamman kan jini da sauran kayayyakin da likitoci suka ce sai an tanada sannan ayi mata aiki a ciro dan, kasancewar ba za ta iya haihuwa da kanta ba.