✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau ’yan Najeriya 1,500 da suka makale a Sudan za su iso Abuja

Za a bayar da fifiko ga kananan yara da dalibai da mata wajen kwaso ’yan Najeriya miliyan uku da ke Sudan

Gwamnatin Tarayya ta ce rukunin farko na ’yan Najeriya da yaki ya ritsa da su a kasar Sudan za su isa Abuja a ranar Juma’a, 28 ga watan Afrilu.

Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare, Abike Dabiri-Erewa ta ce “Muna sa ran isowar ’yan Najeriya 1,500, wadanda jirgin kamfanin Air Peace zai kwaso su daga kasar Masar su iso ranar Juma’a,” in ji ta a ranar Alhamis.

Shi ma da yake jawabi a wata munasabar, kakakin Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Ezekiel Manzo, ya tabbatar da cewa a ranar Juma’a rukunin farko na ’yan Najeriyan da suka makale a Sudan za su fara sauka a Abuja.

Abike ta bayyana cewa za a bayar da fifiko ga mata da kananan yara da dalibai daga cikin ’yan Najeria miliyan uku da ke Sudan kuma gwamnati na yin iya kokarinta domin kwaso su zuwa gida.

Ta kara da cewa, “Manyan bas 13 sun riga sun kama hanyar iyakar kasar Masar da ke Aswan inda Jakadan Najeriya da Darakta-Janar na hukumar NEMA da jami’ansa za su tarbe su.”

Ta bayyana a wani hirar talabijin a tashar Channels cewa wasu jami’o’in Najeriya sun yi tayin daukar daliban da suka dawo daga Sudan domin ci gaba da karatunsu a gida.

An yi watsi da dalibai a tsakiyar sahara

Rahotanni sun bayyana cewa direbobin motoci biyar da suka fara kwasar daliban Najeriya daga Khartoum sun yi watsi da su a cikin sahara na tsawon awa biyar, saboda dambarwar biyan su kudin shatar da aka dauke su.

Iyayen wasu daga cikin daliban sun turo wa wakilinmu bidiyo da muryoyi da ’ya’yan nasu suka turo musu, suna bayanin cewa tafiyarsu daga Khartoum zuwa Aswan ta gamu da cikas.

“Direbobin sun shaida mana cewa kamfanin da suke wa aiki ya umarce su da su dakatar da tafiyar sai an cika musu kudin aikin,” in ji su.

Amma sun ce direbonin sun shaida musu cewa an ba su kafin alkalamin kashi 30 na kudin aikin bisa alkawarin za a cika musu idan suka isar da daliban.

Daliban sun kuma yi korafin rashin abinci a tsawon tafiyar da suka shafe kimanin awa 12 kafin direbobin su yi watsi da su a tsakiyar daji.

An sasanta

Daga bisani dai Abike ta ce hukumar NEMA ta bayyana cewa an daidaita da direbobin sun kama hanyar isar da daliban zuwa kasar Masar.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Franca Omayuli, ta yi zargin kanzon kurege a bayanan da daliban suka yi, tana mai cewa gwamnati na kokarin tabbatar da cewa an kwashe dukkansu daga Sudan cikin mutunci.

Shi ma kakakin NEMA, Ezekiel Manzo, ya karyata batun rashin abincin, da cewa an yi tsarin ciyar da su.

’Yan Najeriya 637 aka kwaso —Ofishin Jakadanci

Ofishin Jakadancin Najeriya a Sudan dai ya sanar cewa sabanin da aka samu kan biyan kudin motocin ya kawo tsaiko wajen kwaso daliban da ke can.

Amma ya ce zuwa ranar Alhamis an kwashe ’yan Najeriya 637 daga Khartoum a cikin motoci 13.

“Duk da cewa kamfanin ya yi alkawarin ba mu motoci 2o a kowace rana, amma daga baya ya janye cikon motoci bakwai da ya turo mana da yama sabo batun biyan kudi, bayan tattaunawarsu da Darakta-Janar na NEMA ba ta yi nasara ba.

Rashin tabbas

“Bisa dukkan alamu kamfanin ya ba da motoci 13 ne, daidai da Dala 400,000 da muka biya… da alama ci gaba da tafiyar ba za ta yiwu ba sai an kammala tattaunawa da su,” in ji wani bangare na wata wasika da ofishin ya rubuta. 

A ranar Alhamis Ofishin Jakadancin kasar Saudiyya da ke Abuja ya sanar cewa Saudiyya ta kwashe wasu mutum 2,544 da suka fito daga kashe 75 daga Sudan,  cikinsu har da wasu ’yan Najeriya 10. Daga cikinsu kuma akwai ’yan Saudiyya mutum 119.

Daga Sagir Kano Saleh, Joshua Odeyemi, Adam Umar, Muideen Olaniyi & Abbas Jimoh