✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata duniya ta hukunta Rasha saboda mamaye kasarmu – Zelenskyy

Ya bayyana hakan ne a jawabinsa yayin taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta hukunta Rasha saboda mamaye kasarsa.

Zelenskyy ya kuma roki majalisar da ta kafa wata kotu ta musamman da za ta kwace kujerar da Rashar take da ita a Kwamitin Tsaro na Majalisar.

Ya bayyana hakan ne a wani jawabinsa da aka nada ta bidiyo kuma aka watsa yayin babban taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 (UNGA-77), ’yan sa’o’i bayan Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya umarci a tura karin dakaru 300,000 zuwa Ukraine, wata bakwai bayan ya mamayeta.

Zelenskyy ya ce, “An aikata laifin yaki a kan Ukraine kuma muna bukatar a yi mana adalci a kuma hukunta ta.”

Sanye da rigarsa mai launin kakin sojoji, Shugaba Zelenskyy ya kuma gabatar da muhimman kudurori guda biyar da za a yi amfani da su wajen hukunta Rashar da kuma farfado da martabar kasarsa.

“Rasha ta cancanci hukunci saboda laifin keta ’yancinmu, hukunci saboda yi wa alfarmar kasarmu kutse. Ya kamata wannan matakin ya ci gaba har sai ta dawo mana da yankunan da ta kwace wadanda duniya ta san da su,” inji Zelenskyy.

Daga cikin tawagar kasar da ta halarci taron har da mai dakinsa, Olena Zelenska.

Wannan dai shi ne karon farko da Zelenskyy ya yi wa Shugabannin duniya jawabi tun bayan da Rasha ta mamaye kasarsa a watan Fabrairu.

Kasashe da dama dai sun mike tsaye suna tafi don nuna goyon baya, bayan kammala jawabin nasa, kodayake wakilan Rasha ba su mike ba.