✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya Kashe ’Yan Mata 3 ’Yan Gida 1 A Yawon Sallah A Nasarawa

Yatake su da mota a yayin da suke komawa gida daga yawon sallah da suka je gidan kanin mahaifinsu

Wani da ake zargin ya yi mankas da giya a lokacin da yake tuki ya hallaka wasu ’yan mata uku ’yan gida ɗaya a yayin da suke tsaka da yawon Sallah a Jihar Nasarawa.

Mutumin da ake zargin ya yi tatul da barasa ya kashe ’yan matan da iyayensu ke Anguwar Baiyi a Karamar Hukumar Toto ne da yammacin ranar Juma’ar da ta gabata.

Wani dangin mahaifin ’yan matan mai suna Saidu Alhassan ya shaida wa wakilinmu cewa yaran, Nusaiba, Maryam da Rumaisa sun je yawon sallah gidan kanin mahaifinsu ne suna dawowa hatsarin ya rutsa da su.

Ya ce “Abin ya faru da yaran ne daf da Fadar Ohinoyi, suna tafiya a gefen titi sai mashayin da ke tsala gudu ya bi ta kansu, nan take kuma suka ce ga garinku nan”.

Suleiman Ozakwo, mahaifin yaran su ya ce hakika mutuwar yaran nasa ta zo a lokacin da ba a yi zato ba, amma babu wanda ya isa ya ja da yin Allah.

Suleiman Ozakwo ya bukaci a saka ‘ya’yan nasa cikin addu’a, yana mai fatan Allah Ya gafarta musu.

Wani dan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar mana da cewa wanda ake zargin, na tsare a hannunsu kuma za su yi abin da ya dace.

Fusattun jama’ar gari sun kone motar da ta yi ajalin yaran.