✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kafa makerar Sabo-Ibadan fiye da shekara 70 baya

Unguwar Sabo-Ibadan ita ce Unguwar Hausawa mafi dadewa a birnin Badun na Jihar Oyo, wadda ta kafu fiye da shekara 100 da suka gabata. Binciken…

Unguwar Sabo-Ibadan ita ce Unguwar Hausawa mafi dadewa a birnin Badun na Jihar Oyo, wadda ta kafu fiye da shekara 100 da suka gabata.

Binciken Aminiya ya gano cewa bayan kafuwar unguwar, wadansu masu sana’ar kira daga cikin Hausawan sun nemi shugabannin unguwar su ba su fili domin su gina wurin sana’arsu ta kira, kuma Sarkin Hausawa na wancan lokaci, marigayi Alhaji Audu Dunguru, ya amince da bukatarsu, ya ba su babban fili suka gina makerar, wacce har yanzu ake kira a cikinta, sama da shekara 70.

Sarkin Makeran Ibadan, Alhaji Muhammadu Sani Gada, mai shekara 73, ya zagaya da Aminiya cikin makerar, inda ya bayyana tarihin kafuwarta.

“Mahaifina mai suna Is’haq Mazawaje, makeri ne da ya fito daga gidan makera da ke kusa da ganuwar garin Kunya, a Karamar Hukumar Minjibir ta Jihar Kano.

Samuwar makerar Sabo-Ibadan

“Bayan shekaru kadan da kafuwar Unguwar Sabo-Ibadan, a tsakanin 1940 zuwa 1947, lokacin yakin Hitler ne mahaifina ya jagoranci takwarorinsa biyu, Malam Adamu da Malam Lukmanu, suka je gaban Sarkin Hausawa na wancan lokaci, marigayi Alhaji Audu Dunguru, domin neman alfarmar filin gina makerar da za su rika yin sana’arsu ta kira.

Daya daga cikin makeran yana kammala kirar wukar fawa

“Sarkin Hausawan ya amince da ba su makeken fili cikin daji (a wancan) lokaci, wanda wannan wuri ne suka gina makerar farko a unguwar ta Sabo-Ibadan.

“Allah Ya yi wa mahaifina arziki. Da sana’ar kira ya yi aure ya gina gidajen da ya rasu ya bar mana gado ni da yayana marigayi Bashiru.

Abin daya sa aka raba makerar

“Sai dai bayan rasuwar mutum biyu da suka gina makerar tare da mahaifina sai danginsu daga jihohin Neja da Nasarawa suka zo neman hakkin iyayensu, wanda shugabannin gari suka raba makerar aka sayar da wani bangare ga jama’a, aka mika musu rabonsu.

“Sauran ginin makerar ce kake gani ana amfani da shi a matsayin rabon ’ya’yan Is’haq Mazawaje, wato mahaifina.

“Daga nan ne mahaifina ya samo wani mataimaki mai suna Malam Saleh suka ci gaba da sana’ar kere-kere domin raya kira a wannan sashe na Najeriya,” inji shi.

Nadin Sarkin Makeran Sabo-Ibadan

Sarkin Makeran Ibadan, Alhaji Muhammadu Sani Gada

Ko yaya aka yi ya zama Sarkin Makeran Ibadan kuma wane tasiri ko amfani ke tattare da wannan sarauta?

Sarkin Makeran ya bayyana cewa a shekarar 2010 ne Masarautar Hausawan Ibadan, a karkashin Sarkin Hausawa Ahmad Dahiru Zungeru (Jikan Sarki Audu Dunguru) ta yanke shawarar nada hakimai daga gidajen Hausawan da suka yi gadon wasu sana’o’i, kamar kira da fawa da wanzanci.

“A wannan lokaci ne mutanenmu masu sana’ar kira suka amince da bayar da sunana a matsayin Sarkin Makera.

“Mun gayyaci ’yan uwa makera daga Arewa zuwa wajen nadin sarautar, inda muka yi bukukuwa da wasannin al’adun gargajiya, irin wadanda muka yi gado kaka da kakanni.

“Daruruwan kabilu da ke zaune a Badun, musamman malaman manyan makarantu da manyan mutane sun kalli irin wasannin al’adu da mutanenmu suka yi a wancan lokaci.

Fa’idar saurautar Sarin Makera

“Wasu daga cikin amfanin sarautar sun hada da kyautata zamantakewar mutanena da sauran jama’ar gari da lalubo hanyar daukaka darajar sana’ar kira da fafutukar kusantar mahukunta domin samun tallafin da suke bayarwa ga masu sana’o’i”, inji shi.

Wakilin Aminiya ya tambayi Sarkin Makera ko shi da kansa yana yin kira a yanzu?

Sai ya ce: “Wani kakanmu mai suna Zubairu Baba Agwa dan boko ne da ya taba yin aiki a matsayin babban malamin makarantar firamare ta Unguwar Sabo da aikin gidan rediyon Redifusion na Ibadan, shi ne ya shawarci mahaifinmu ya sanya mu a makarantar allo da ta boko.

“Ka ji dalilin da ya sa mahaifinmu Is’haq Mazawaje bai koya mana sana’ar kira ba; a dalilin aiki da wannan shawara.”

Albarkar sana’ar kira

Aminiya ta samu zantawa da Sadi Garba, daya daga cikin masu sana’ar kira a wannan makera, wanda ya ce tun yana karami ya koyi kira daga iyayensa a garin Bunkure, Jihar Kano.

“Duk da bullar kirar zamani, akwai riba da rufin asiri sosai a wannan sana’a ta kirar gargajiya mai dogon tarihi da Allah Ya sanya mata albarka.

“Muna kera wukaken da mahauta ke amfani da su da askar da wanzamai ke aski da adduna kuma akwai wadanda suke ba mu kwangilar kera kayan noma kamar fartanya da sauransu.

“Mu ma a wannan sashe har yanzu muna yin wasannin al’adun gargajiya da muka yi gado domin nuna irin baiwar da Allah Ya yi mana.

Ala’adu da kayan kira

“Irin su wasannin wuta da muke yi a yanzu sun hada da sanya wuta cikin baki da cinna wuta a gashin kai da goga wuta a tafin kafa ba tare da ta yi mana komai ba”, inji shi.

Sadi ya nuna wa Aminiya kayan aikinsu da suka hada da gudumar bugun karfe da arabtaki da zarton wasa wuka da gizagon sassakar itace da kurfin sara karfe da masaba da makera da ake sarrafa karfe a kanta da zuga-zugin hura wuta da sauransu.

Kasuwar kayan makera

Shi kuwa Umar Awwalu sayar da kayan da makera suka sarrafa yake yi.

“Ba mu muke kera kayan ba, muna saye ne daga hannun makeran mu shiga cikin kasuwanni a garuruwa da kauyukan Kurmi baki daya domin sayarwa ga mabukata.

“Sai dai zamani ya cim mana inda abubuwa suka canja aka samu karancin kasuwa in aka kwatanta da shekarun baya kafin bullar kayan kira na zamani.

“Amma mun gode Allah, ana samun abin rufin asiri. Ina so ’ya’yana su gaje ni a kan wannan sana’a, musamman a wannan lokaci na rashin aikin yi”, inji shi.

Takurar gwamnati saboda tsaro

Amma Dauda Sule cewa ya yi, “A yanzu mun shiga cikin wani yanayi da ya haifar da barazana gare mu da muke shiga cikin jama’a dauke da makamai, dalilin rashin tsaro a kasa.

“Jami’an tsaro suna takura mana a kan hanya da kasuwanni saboda daukar irin wadannan kaya da muke sayarwa a bayyane ga jama’a.

Muna kira ga mahukunta su dauki matakin kyale mu mu yi sana’armu da muka dogara da ita wajen cin abinci.

“Kamata ya yi gwamnati ta yi alfahari da girmama sana’ar kere-keren abubuwan cikin gida ba tare da an shigo da su daga kasashen ketare ba.

Bukatar kwarin gwiwa daga gwamnati

“Amma a maimakon a karfafa mana gwiwa mu kai ga kera abubuwan da suka fi wadanda muke kerawa yanzu, sai takura mana ake yi.

“Kuma wani abin bakin ciki shi ne irin yadda gwamnati ta manta da masu sana’ar kira a shirinta na tallafa wa masu sana’o’in hannu.

“Gwamnati tana taimaka wa wanzamai da mahauta da teloli da sauransu amma an manta da masu kira a irin wannan tallafi da bashin bunkasa sana’a da zai rage matsalar rashin aikin yi da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya kamata gwamnati ta yi wa masu sana’ar kira adalci wajen sanya su cikin jerin masu cin wannan moriya”, inji makerin.