✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi wa Fulani kisan gilla a Anambra

Kungiyar IPOB ta yi wa Fulani 19 ’yan gida daya kisan gilla a Jihar Anambra.

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar IPOB ne sun yi wa wasu Fulani 19 makiyaya ’yan gida daya yankan rago a Jihar Anambra.

Shugaban Kungiyar Cigaban Fulani ta Gan Allah, Alhaji Suleiman Yakubu, wanda surukin mai gidan da aka kai hairn ne ya ce mutum daya ne kacal ya tsallake rijiya da baya a harin na kauyen Igbariam da ke Karamar Hukumar Oyi ta Jihar.

Ta yaya aka samu labarin abin daya faru a Jihar Anambra?

Ranar Litinin, 26 ga Afrilu ne aka kira ni da tsakar dare cewa an kai hari gidan Ibrahim Medium an kashe shi da iyalansa mutum 19.

Abin ya faru ne ranar Lahadi da dare, aka kira ni da misalign karfe biyu kafin wayewar garin Litinin cewa ’yan kungiyar IPOB sun kai hari a gidan, mutum daya ne kawai ya tsira.

Wanda ya tsiran shi ma ba ya gidan ne a lokacin da aka kai harin. Yana dawowa sai ya ji muryar maharan a gidan, sai ya buya.

Da suka tafi ne ya shiga gidan ya samu duk an kashe su an kashe dabbobin gidan.

Dabbobin na killace a wurin da babu hadari ga maharan, amma hakan bai hana a sassare su, a kashe wasu da dama.

Yaya yanayin wurin yake yanzu?

Na yi magana da wani babban mutum da ke can, ya ce min da wuya iyalan matan da aka kashe su yafe wa maharan.

Amma a bangarenmu, muna yin iya kokarinmu wajen kwantar da hankalinsu.

Amma abin da aka yi musu tsantsar rashin imani ne.

 

Mata nawa ne aka kashe?

An kashe mata tara, kananan yara shida, sai wani tsoho (Ibrahim) da wasu maza uku. Ibrahim ya dade yana zaune a wurin.

 

Shin kun kai wa jami’an tsaro rahoto?

Mun sanar da su, amma har yanzu ba su ce mana komai ba.

Yanzu a wani hali Fulanin da ke wurin suke ciki?

Fulani na cikin zaman dar-dar sabodon abin da ke ta faruwa a yankin Kudu-maso-Gabas.

Duk da cewa wasu na ganin ko da za a ce wasu su tashi, to banda su, saboda dadewar da suka yi suna zaune a wurin.

Sun dade suna zama da yin hulda da mutanen yankin har sun koyi al’adunsu, sai dai kuma yanzu su ake ta zagi, babu wanda ya san me zai biyo baya.

Duk Bafulatanin da ke zaune a jihar a tsorace yake, wasu ma sun riga sun bar jihar.

 

Mutumin da aka kashe, Ibrahim Medium, ya yi shekara nawa yana zama a wurin?

Tabbas, ya sha yin alfahari da cewa yana zaune cikin aminci a wurin, kuma ba yadda za a yi a tashe shi a wurin saboda dadewar da ya yi yana zaune a wurin.

Kafin rasuwarsa, yana kallon kansa a matsayin dan asalin wurin saboda shekara 25 ya yi yana zaune a wurin.

Abbas Dalibi, Ibadan, Faruk Shuaibu da Sagir Kano Saleh