✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake miyar dage-dage

Ba miya ce wadda za a yi ta cikin sauri ba, sannan a yi tsammanin za ta yi dadi ba.

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri. Miyar dagedage miya ce wadda ake yin ta a tsanake.

Ba miya ce wadda za a yi ta cikin sauri ba, sannan a yi tsammanin za ta yi dadi ba.

Yadda wata za ta yi tata miyar daban ya ke da yadda wata za ta yi miyar dage-dagen.

Sannan akwai kurakurai da mata ke tafkawa wajen yin wannan miyar.

Idan lokacin bikin Sallah ya yi nan ne fa za’a ga irin miyar da ake kawowa daga makwabta.

Wata miyar ko dandana wa ba za a iya yi ba saboda tsabagen tsami da kuma danyenta.

Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a yi wannan miyar a tsanake.

Abubuwan da za’a bukata

·        Timatir manya 10

·        Tattasai kanana hudu

·        Attarugu 5

·        Albasa karama daya

·        Ganda

·        Kaza

·        Nama

·        Kori

·        Tafarnuwa

·        Man gyada ko Man ja Hadi

Da farko za a wanke wannan kayan miyar da na lissafo sannan a markada su. Daga nan sai a wanke kaza da nama da ganda a silalasu har sai sun yi laushi. Sai a ajiye a gefe.

A daura markaden kayan miya a wuta ya yi ta tafasa har sai ruwan ya tsane.

Sannan a zuba Man gyada ko Man ja ayi ta soyawa har sai man gyadar ya hauro samar kayan miya.

Sannan a dauko romon nama a zuba tare da naman sai a gauraya.

A zuba su Magi da Kori da kuma garin Tafarnuwa sannan a sake gauraya wa.

A rufe na tsawon mintuna biyu sannan a dandana a ji in da tsami.

Idan da tsami sai a jika Kanwa kadan sosai a ruwa sannan a zuba kamar murfin goran Fanta sannan a gauraya idan miyar ta nuna sai a sauke a ci da farar shinkafa.