✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ake Yin ‘Yam Balls’

Ana iya yin ‘Yam Balls’ a matsayin abinci, ko kuma don marmari, ko na tarbar baki ko kuma a matsayin abincin sana’a.

Kayan hadi

  1. Doya
  2. Attarugu
  3. Albasa
  4. Kwai
  5. Magi
  6. Gishiri
  7. Kori
  8. Mai

Yadda ake hadawa

  1. A fere doya a yanka ta sai a wanke a sa a tukunya a dora a wuta da dan gishiri.
  2. Idan ya nuna sai a sauke a kawo turmi mai tsafta a daka doyar sama-sama.
  3. Sai a dauko jajjagen attarugu, albasa, sunadarin dandano da kori a zuba a kan doyar a juya su hadu sosai.
  4. Daga nan sai a rika dunkula doyar a yi ta kamar kwallo.
  5. Sai a fasa kwai a dora kasko a wuta a sa mai.
  6. Idan man ya yi zafi sai a rika dauko kwallon doyar ana tsomawa a kwai ana soyawa a man.
  7. Idan ya yi sai a kwashe.

Shi ke nan sai ci.