✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Jana’izar Sarauniya Elizabeth Za Ta Gudana

Sabon Sarkin Ingila, Charles III zai gana da Fira Minista Liz Truss ranar Juma'a

Sabon Sarkin Ingila, Charles III zai yi wata ganawa da Fira Minista Liz Truss, ranar Juma’a gabanin jana’izar Sarauniya Elizabeth II.

Tuni aka fara tsare-tsaren gudanar jana’izar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, wadda ta rasu ranar Alhamis a Fadar Balmoral sakamakon jinya, tana da shekara 96 a duniya.

A ranar Juma’a Charles da matarsa Camilla, wadanda suka kwana a Fadar Balmoral, za su wuce zuwa birnin London, inda zai gana da Fira Minista Liz Truss.

Charles ya zama sarki ne kai-tsaye bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II.

Ranar Asabar za a nada shi a hukumance bayan zaman majalisar Masarautar Ingila a Fadar St James’s da ke birnin London.

Yadda za a yi jana’izar Sarauniya Elizabeth II

Da yake tabbatar da gudanar da jana’izar Sarauniya Elizabeth II, ana sa rana Sarki Charles III zai gana da Duke na Norfolk, Earl Marshal, wanda ke da alhakin jagorantar jana’izar Sarauniya.

Shi ne basaraken da ke da hurumin sahale irin tsarin da za a bi a kwanaki masu zuwa.

Zaman makoki na kasa

A nan gaba Gwamnatin Birtaniya  za ta ayyana zaman makoki na kasa saboda rasuwar Sarauniya Elizabeth, wanda tsawonsa ke iya kaiwa kwana 21 around 12 days, wato daga yanzu har zuwa washegarin ranar da za a kai ta makwancinta.

Tuni dai jama’ar suka fara yin tururuwa zuwa Fadar Buckingham da sauran gidajen sarauta domin ajiye furannin nuna jimami game rasuwar Sarauniya da ta shekara 96 a duniya.

Ministoci kuma za su ayyana ranar jana’izar a matsayin ranar hutun aiki a kasar Birtaniya.

Makokin Gidan Sarauta

Sarki Charles zai ayyana tsawon lokacin makokin da Majalisar Masarautar za su yi, tare da daukacin iyalan gidan sarautar.

Ana kyautata zaton tsawon nasu makokin da zai ayyana zai iya kaiwa wata guda.

A halin yanzu dai an yi kasa-kasa da tutocin Masarautar Birtaniya a daukacin gidajen sarautar.

Za kuma a kada kararrawa a Westminster Abbey, Cocin St Paul’s Cathedral da Fadar Windsor.

An kuma bukaci coci-coci da ke fadin yankin Ingila da su ma su kada kararrawa da misalin karfe 12 ba rana.

Harbin bindiga 96

Za a harba bindiga sau 96, daya ga kowane shekara da Sarauniya Elizabeth II ta yi na tsawon rayuwarta a doron duniya.

Shi dai wannan Harbin bindiga za a gudanar da shi ne a Dandalin Hyde Park da wasu wuraren.

Jawabin Sarki Charles A Talabijin

Sarki Charles III zai gabatar da jawabi ga al’ummar Birtaniya ta talabijin.

Da misalin La’asar dai ake sa ran nadar jawabin nasa kafin daga baya a sanya a gidajen talabijin.

A jawabinsa, zai yi jinjinar bangirma ga Sarauniya, sannan ya dauki alkawarin yin aiki tare da sauke nauyin da ya rataya a kansa a matsayin sabon Sarki.

Ibadar jana’iza a St Paul’s

Ana sa ran Fira Ministar Birtaniya, Liz Truss tare da manyan ministocin kasar za su halarci ibadar jana’iza da bankwana a cocin St. Paul’s da ke kwaryar birnin London.