✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka sasanta aka sako Daliban Kankara ba biyan kudin fansa

Gwamnan Zamfara ya ce a hannun ’yan bindiga aka karbo yaran ba Boko Haram ba

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana yadda ya sasanta da ’yan bindiga suka saki ’yan Makarantar Sakandaren Kimiyya da ke Kankara, Jihar Katsina da suka sace ba tare da an biya ko sisin kwabo ba a matsayin kudin fansa ba. 

’Yan ta’adda ne suka yi garkuwa da su a ranar Juma’a, 11 ga watan Disambar 2020 a makarantarsu da ke garin Kankara, Jihar Katsina.

Duk da cewa kungiyar Boko Haram ta bayyana dauki alhakin garkuwa da yaran da ta ce su 524 ne, Gwamnatin Jihar Katsina a ranar Alhamis ta ce daliban guda 344 ne masu garkuwar suka sako.

A zantawar da ya yi da Daily Nigerian, wata jaridar intanet, Gwamna Matawalle na Zamfara ya bayyana cewa ya yi amfani da tsofaffin shugabannin ’yan ta’addar da na kungiyar Fulani ta Miyetti Allah don yin sulhu da lallashin masu garkuwar.

“Na bukace su da su saki yaran ba tare da sun samu lahani ba kuma sun yi hakan a daren jiya.

“Ba wannan ne karo na farko ba da muka shiga tsakani aka saki mutanenmu da aka yi garkuwa da su ba tare da an biya kudin fansa ba.

“Ina tabbatar wa kowa, cewa ba mu biya ’yan bindigar ko sisin kwabo ba; Abun da muka yi shi ne ba su dama domin su ma suna son su zauna lafiya.

“Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa Tsafe daga india suke, inda za su zo su dan huta, su yada zango a Gusau su kwana.

“Da safe kuma Juma’a su kama hanyarsu ta zuwa Katsina,” inji gwamna Matawalle.

Game da ikirarin ’yan Boko Haram na garkuwa da yaran, Matawalle ya ce ba kungiyar ba ce ta yi garkuwa da daliban.

“Sam babu wani abu mai kama da Boko Haram a wannan lamarin; ’yan bindiga ne suka yi garkuwa da su,” inji gwamnan.

Ya ce sulhu ne kadai zai kawo karshen ayyhkan ’yan bindiga a yankin Arewacin Najeriya.

“Idan da gwamnoni za su zauna su fuskancin matsalolin ta hanyar masalaha to akalla za a rage ayyukan na ’yan ta’adda,” inji shi.

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa shigar harkokin siyasa cikin lamarin na daga cikin dalilan da ke kara bayar da matsala.

“Tabbas zan iya fada maka jami’an tsaron da suke kokari kwarai da gaske.

Ya ce: “Idan muka cire tsoma siyasa da katsalandan cikin lamarin, za a samu sakamako mai kyau,”