✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rasuwar mahaifin Ali Nuhu ta girgiza Kannywood

Rasuwar mahaifin Ali Nuhu, fitaccen jarumi kuma darakta a masana’antar Kannywood, Nuhu Poloma, ta jefa masana’antar cikin jimami. Ranar Litinin ne mahaifin jarumin, wanda ake…

Rasuwar mahaifin Ali Nuhu, fitaccen jarumi kuma darakta a masana’antar Kannywood, Nuhu Poloma, ta jefa masana’antar cikin jimami.

Ranar Litinin ne mahaifin jarumin, wanda ake yiwa lakabi da Sarki Ali, ya rasu.

Mamacin, wanda tsohon dan siyasa ne, ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya.

Shi dai Nuhu Poloma wanda dan karamar hukumar Balanga ne ta jihar Gombe, na cikin fitattun ‘yan siyasa a jihar na tsawon lokaci.

Aminiya ta ruwaito rasuwar mamacin daga shafin furodusa Naziru Danhajiya, wanda daya ne daga cikin makusanta Ali Nuhu a Kannywood.

Kannywood na ta’aziyya

Naziru ya wallafa a shafinsa cewa, “Inna Lillahi wa inna ilaihirrajiun. Allah Ya yi wa mahaifin Ali Nuhu rasuwa yanzu a Gombe.”

Manya da kananan jaruman masana’antar sun biyo baya wajen yin ta’aziya ga Ali Nuhu.

Abokin Ali Nuhu kuma fitaccen jarumi, Yakubu Muhammed, ya ce, “Ali Nuhu ya yi rashin mahaifinsa.

“Muna addu’ar Allah Ya jikansa. Muna mika ta’aziya a gare ka.

“Allah Ya ba ka hakurin [jure wannan] rashi, dan uwa.”

Matashin furodusa Alhaji Khalid Yusuf Ata cewa ya yi, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah Ya ba ka ikon juriya.”

Wallafa hotuna

Mahaifin Ali Nuhu, marigayi Nuhu Poloma

Fitaccen furodusa, Abubakar Bashir Maishadda, wanda yanzu kusan shi ne na hannun daman Ali Nuhun da kuma suka yi fina-finai da yawa tare, ya wallafa hotonsa tare da Ali Nuhu sannan ya ce, “Allah Ya ba ka juriya da hakurin [jure wannan] rashi daraktana”.

Ita ma tsohuwar jaruma Fati Muhammed, wadda ta dade tare da Ali Nuhu, ta ce, “Tabbas yayana ka yi babban rashi na mahaifi.

“Allah Ya sa idan namu lokacin ya yi mu cika da imani. Kai kuma Allah Ya ba ka hakuri da juriyar rashin, amin.”

Sauran wadanda suka yi ta’aziyya sun hada da darakta Sanusi Oscar 442 da jarumi Adam A. Zango da darakta Aminu S. Bono da jarumai Teema Makamashi da Halima Atete da sauransu, inda suka yi ta sanya hoton jarumin ko na mamacin ko kuma sake yada wanda wasu suka sanya.