✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ta kaya a manyan wasannin Firimiyar Ingila na karshen mako

Cikin yamutsin har da bakuncin Chelsea da Aston Villa ta karba a Villa Park.

A ranar Lahadin da ta gabata manyan kungiyoyin kafar Ingila suka fafata a wasannin mako na 11 na gasar Firimiyar Ingila ta bana.

Wasannin dai sun hada da yamutsin da Aston Villa ta karbi bakuncin Chelsea a Villa Park, sai gumurzun da aka yi tsakanin Manchester United da Newcastle a Old Trafford da kuma karon battan da aka yi tsakanin Arsenal da Leeds United da kuma fafatawar da aka yi a gidan Liverpool tsakaninta da Manchester city.

Mason Mount ya yi bajinta a karawar Chelsea da Aston Villa

Chelsea ta doke Aston Villa da ci 2-0 a wasan mako na 11 a gasar Firimiyar Ingila da suka kara ranar Lahadi a Villa Park.

Minti shida da fara wasa, Chelsea ta zura kwallo a raga ta hannun Mason Mount, shi ne ya kara na biyu a zagaye na biyu a karawar.

Wannan shi ne karo na uku da Mount ya ci kwallo biyu ko fiye da haka a Firimiyar Ingila da yake yi wa Chelsea.

A kakar 2021 cikin watan Oktoban, Mason ya ci Norwich City uku, sannan ya zura biyu a ragar Southampton cikin watan Afrilun 2022.

Sabon koci, Graham Potter ya ci wasa uku a jere da fara jan ragamar Chelsea a Firimiyar Ingila a kakar nan, tun bayan da ya maye gurbin Thomas Tuchel.

Da wannan sakamakon Chelsea wadda ta yi wasa takwas a babbar gasar tamaula ta Ingila, tana ta hudu a teburin Firimiyar da maki 16.

Ranar 19 ga watan Oktoba, Chelsea za ta ziyarci Brentford a wasanta na gaba a Firimiyar Ingila.

Ita kuwa Aston Villa za ta ziyarci Fulham ranar Alhamis 20 ga watan Oktoba.

United ta yi canjaras da Newcastle

Manchester United ta tashi 0-0 a wasan mako na 11 a gasar Firimiyar Ingila da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi.

Kungiyoyin sun samu damar makin zura kwallo a raga tun farko, musamman Newcatle da kwallo biyu ya bugi turke.

Marcus Rashford ya samu dama mai kyau a karshen lokaci, wanda ya sawa kwallo kai ta yi fadi ta fita waje.

Karon farko da sabon koci, Erik ten Hag ya tashi 0-0 a dukkan wasan da ya ja ragamar United kawo yanzu a bana.

Kociyan ya ja ragamar wasa 13 a dukkan fafatawar da United ke yi a kakar 2022/23 kawo yanzu.

Cristiano Ronaldo ya buga wasan, wanda daga baya Rashford ya canja, an kuma ga kyaftin din Portugal na jijjiga kai a lokacin da zai fita daga filin.

Da wannan sakamakon Manchester United wadda ta yi wasa tara tana da maki 16, ita kuwa Newcastle tana da 15 biye da kungiyar Old Trafford.

Ranar Laraba 19 ga watan Okboba, Manchester United za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan da zai yi zafi.

A kuma ranar Newcastle United za ta yi wa Everton masauki a St Jamrs Park.

Liverpool ta yi wa City ci daya mai ban haushi

Kwallo daya tilo da Mohamed Salah ya jefa a ragar Manchester City, ta kawo karshen jerin nasarorin da tawagar Pep Guardiola ta rika samu a wasannin da ta rika bugawa tun farkon kakar wasa ta bana.

Arsenal ta samu gindin zama a teburin Firimiyar

Rashin nasarar ta farko da City ta yi a bana, ta bai wa Arsenal damar ci gaba da zama a saman tebur gasar Firimiyar, bayan da Gunners din suka samu nasarar doke Leeds United da kwallo 1-0 a karawar da suka yi ranar Lahadi.