Daily Trust Aminiya - Yadda ’yan bindigar Katsina suka mika makamansu
Subscribe
Dailytrust TV

Yadda ’yan bindigar Katsina suka mika makamansu

Daya daga cikin jagororin ’yan bindigar da suka addabi Jihar Katsina, mai suna Ado Sarki, ya bayyana tubansa tare da mika wa gwamnati makamansa.

Ado da yaransa na daga cikin masu addabar Kananan Hukumomin Safana da Batsari, yankunan da hare-haren ’yan bindiga suka yi wa mummunar illa a Jihar.

Ado wanda ya jagoranci wadansu daga cikin yaransa wurin mika makaman, ya yi alkawarin cewa sun yi hannun riga da ayyukan ta’addanci, ko da a bakin ransu ne.

Ga dai abin da Adon ya ce a lokacin mika makaman ga Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, CP Sanusi Buba.