✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan Najeriya ke caccakar Buhari kan satar Daliban Kaduna

Sabon gargadinsa ga ’yan bindiga da umarnin a ceto daliban ya ja mishi caccaka.

’Yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari rubdugu kan garkuwa da aka yi da dalibai 39 a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya (FCFM) da ke Kaduna. 

Masu sharhi sun fara caccakar Shugaban Kasar ne bayan ya ba da umarnin a gaggauta ceto daliban tare da gargadin yan bindiga da ke addabar makarantu su shiga taitayinsu.

A sanarwar da kakakinsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar kan garkuwa da daliban da aka yi a daren Juma’a, Buhari ya ce ba zai lamunci miyagu su gurgunta harkar makarantu ba a Najeriya.

Fitar sanarwar ta Garba Shehu a Twitter ke da wuya aka fara yi masa raddi inda @ElafikuwSunday ya ce, “Ai Buhari ya yi irin wannan gargadi sau shurin masaki amma ba abin da ya sauya. Me zai hana ku bi su kuma gama da su baki daya? Ko dai ba ku gaji da ba da gargadi ba ne?”

Kashedin na Buhari na zuwa ne bayan masu garkuwar sun fitar da bidiyon daliban suna neman Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansar su.

A baya dai Shugaban Kasar ya yi alkawarin ba zai sake bari a yi garkuwa da dalibai ba bayan wanda aka yi wa dalibai mata 279 a makarantar sakandaren GGSS Jangebe, Jihar Zamfara.

Daga cikin masu raddi, @dawisu ya yi shagube da cewa, “Gaskiya kuna rikita ‘yan bindiga/’yan ta’adda. Makon jiya a Zamfara kun ba su wa’adin wata biyu, yau kuma kuna musu kashedi mai karfi. Wanne za su dauka da muhimmanci, Malam Garba? Da dana na makarantar kwana a jihohin da hakan ke faruwa da cire shi kawai zan yi.”

@bamydel ya ce, “Kullum sai dai ku yi gargadi ko alkawari, amma kun ce an yi na karshe. Me ke hana ‘yan siyasa nuna sanin ya kamata? Da irin wannan sanarwar gara yin shiru.”

Buhari ya yaba da kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi da kuma yadda sojoji suka yi gaggawar kai dauki, lamarin da ya kai ga ceto dalibai 180 ciki har da ma’aikata takwas.

Ya kuma yaba da gudummawar da ake bayarwa na bayanan sirri da ke taimakawa wajen dakile masu satar mutane, da cewa ingantacciyar sadarwa na taimaka wa kasa ta kasance cikin aminci.

“Duk da makaman da sojojinmu ke da su, amma suna bukatar hazaka wajen kare kasar kuma dole mazauna su tashi a tunkari wannan  kalubalen.”

Shugaba Buhari, wanda ya yi juyayi ga wadanda lamarin ya rutsa da su, ya yi fatan ganin sun kubuta.

Yadda ’yan ke caccakar Buhari ka daliban Kaduna

Fitar sanarwar ta Garba Shehu a Twitter ke da wuya aka fara yi masa raddi.

@Tvezbaba_15 ya ce, “Duk lokacin da Shugaban Kasa ya yi gargadi mai karfi, sai ‘yan bindiga sun kalubalance shi sun kai sabon hari, sai ka ce sun fi shi azama.”

@Idgarba ya ce, “Mista Garba, anya wannan gargadin daga Shugaban Kasa ne kuwa? Ni dai na tabbata Shugaban Kasa ya riga ya yi kashedin karshe. To wannan kuma fa?”