✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan Najeriya suka fusata da kisan manoma a Borno

’Yan Najeriya na kira Majalisa ta fara muhawara, a kori Manyan Hafsoshin Tsaro nan take

’Yan Najeriya sun hasala da kisan gillar da kungiyar Boko Haram ta yi wa wasu manoman shinkafan a Zabarmari, Jihar Borno ranar Asabar.

Yankan ragon da kungiyar ta yi wa manoman a gonaki ya sa ’yan Najeriya musamman a shafukan zumnata kira ga Majalisar Tarayya ta gaggauta fara muhawara a kan batun, wasu kuma na kira da kori  Manyan Hafsoshin Tsaro nan take.

Salihu Tanko Yakasai, hadimin Gwamna Ganduje na Jihar Kano, na daga cikin wadnda suka yi tir da harin da kuma rashin daukar mataki a kai.

“Idan wannan bai sa ka kuka ba to ban san me zai sa ka ba. Mutum 43 su wayi gari a wurin neman halal dinsu, amma kama su a yi musu yankan rago. Amma har aka yi awa 24 babu wanda aka kora daga aikinsa kuma babu wani kwakkwaran mataki da aka dauka; To ba mamaki bayan wasu karin awa 24 korafin ya gushe a ci gaba da harkoki…”

“Haka za a rika wasa da batun ba wa ’yan kasa damar mallakar manyan makamai su kare kan su har sai lokacin magance wadannan kashe-kashe na ba gaira ba dalili ya kure. Lokaci ya yi na @nassnigeria (Majalisar Tarayya) ta fara muhawara a kan wannan lamari”, inji Audu Anuga.

Aminu Ahmed ya ce: “Babu abin da ke sa wadannan abubuwan faruwa face rashin hukunta kowa a kai”.

Tun farkon faruwar lamarin Salihu Tanko Yakasai, ta shafinsa na Twitter, ya ce:

“Inna Lillahi Wa Inna Ilaihirrajiun! An jefa iyalai 43 cikin duhu, an yi asarar karin manoma 43 masu ciyar da kasa, an kashe karin mutum 43 a banza. Alhaki na wuyan wadanda ya kamata su kare rayukansu.

“Ina ganin laifin ’yan Arewa ne da suka lamunci wannan rashin tsaro. Ina jin sai abin ya shafi kowane gida ko dangi za mu yunkura mu magance wannan dabbanci na hare-haren da satar mutane. Babu alamar karewar masalar a nan kusa. #ZabarmariMassacre

“Ba mu ma shirya yin magana da murya daya ba game da rashin tsaro a Arewa. Ba mu ma shirya ba. #SecureNorth”, inji shi.