✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aiki: Gwamnonin APC sun nemi El-Rufai ya sasanta da NLC

Kungiyar ta bukaci El-Rufai da kungiyar su zauna a teburin shawara.

Gwamnonin Jam’iyyar APC sun shawarci Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna ya sasanta da Kungiyar Kwadago (NLC) kan takaddamar da ke tsakaninsu da ya sa kungiyar yajin aik a Jihar.

Kungiyoyin kwadago a Jihar Kaduna sun fara yajin aikin gargadi na kwana biyar ne domin matsa wa gwamnan ya janye sallamar dubban ma’aiakatan jihar da ya yi.

Gwamnan Jihar Kebbi kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Atiku Bagudu ya bukaci NLC da ta nuna fahimta wajen tattaunawa da gwamnati a dukkan matakai.

Bagudu ya ce ganin yadda kasar ke cikin wani yanayi, abin da ya fi dacewa shi ne NLC da Gwamnatin jihar su hau kan teburin sulhu, wajen shawo kan lamarin.

“Duba da matsalolin da jihohinmu ke fuskanta, musamman na karancin kudaden shiga, muna kira ga ’yan kasa masu kishi da su nuna fahimta wajen tattaunawa da gwamnati domin yi wa tufkar hanci. Yanzu ba lokacin tayar da jijiyoyi ba ne.

“Matsaloli sun riga sun yi wa ’yan Najeriya yawa kuma a wannan mataki ba za a iya kayyade matakan tattaunawa tsakanin gwamnatoci da ’yan kasa ba.

“Saboda haka wajibi ne a bi duk matakan da suka dace don magance takaddamar da ke tsakanin Gwamnatin Kaduna da NLC kuma muna kira garesu da su koma kan teburin sulhu,” inji shi.