✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin ASUU: Yadda muke rayuwa ba tare da albashi ba — Malaman jami’a

Malaman sun bayyana irin halin da suka shiga

  • Buhari ya ba Ministan Ilimi mako 2 ya kawo karshen lamarin
  • Mako 2 ba zai yi wani tasiri ba sai dai idan… — ASUU

A daidai lokacin da aka kwashe wata biyar malaman jami’o’in Najeriya suna yajin aiki, malamai da dama sun shiga mawuyacin hali saboda tsarin Gwamnatin Tarayya da jihohi na ba aiki, ba albashi.

An fara yajin aiki na gargadi ne a ranar 14 ga Fabrairu na mako hudu, daga nan aka dora na dindindin har zuwa yanzu.

Wannan ya sa malaman sun kwashe kimanin wata hudu suna zaune a gida ba tare da albashi ba, lamarin da ya jefa wasu daga cikinsu da iyalansu a cikin kunci.

Dokta Rukayya Yusuf Aliyu, malama ce a Jami’ar Bayero da ke Kano ta ce tana amfani da ilimi da kwarewarta ne wajen wasu ayyukan bayar da horo da shawarwari ga wasu ma’aikatu.

Ta ce mijinta ne yake taimakonta wajen rage radadin rashin albashin, “Matan aure musamman wadanda suka auri mazan kwarai da sauki, amma gaskiya malamai maza suna cikin damuwa matuka,” inji ta.

Sai dai ta ce duk wahalar da ake ciki ta amince a ci gaba da yajin aikin har sai an biya musu bukatunsu.

A nasa bangaren, Dokta Muhammad Hashim Suleiman da ke koyarwa a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ya ce gwamnati ba ta bi dokar daina biyan albashin daidai ba.

A cewarsa, “Gwamnati a matsayinta na wadda ta karya doka, sai ta zabi dokar da za ta dabbaka. Dokar cewa ta yi za a daina biyan albashi bayan kwana 90, wato wata uku ke nan.

Amma da fara yajin aikin, sai gwamnati ta yi tunanin za ta hora mu da yunwa. Mun fara yajin aiki, sai su ma ma’aikatan jami’o’in da ba malamai ba suka shiga yajin aikin, amma aka ci gaba da biyan su, amma mu aka daina biyan mu albashi. Ba mu san wace irin doka ba ce suke amfani da ita da take raba tsakanin bangarorin biyu.

“Kowa da yadda ya zabi domin neman hanyar ciyar da iyali. Wasu na dan taba kasuwanci, wasu na noma, sannan ita kanta kungiyar ASUU tana da wani tsari na taimakon mambobinta,” inji shi.

Sai dai Malam Abdullahi Ibrahim na Jami’ar Tarayya da ke Wukari cewa ya yi da bashin da yake karba daga abokai yake rayuwa.

Ya ce “Rayuwa ta yi wahala sosai. Sai dai ina dan taba noma abin da muke ci, sauran kuma bashi nake ci domin biyan bukatun rayuwa.”

Sai dai shi ma ya ce duk da wahalar da yake ciki, ya amince a cigaba da yajin aikin har sai gwamnati ta biya musu akalla kashi 60 na bukatunsu. Malam Nuhu Mohammed na Jami’ar Tarayya da ke Gusau ya ce su kansu ba san jin dadin yajin aikin, amma shi ne kadai hanyar da za a saurare su.

Ya ce yana rayuwa ce da dan abin da yake samu daga ’yan uwa da abokan arziki tun lokacin da aka daina biyansu albashi saboda yajin aikin. Shi ma Dokta Ashir Tukur na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce an kawo tsarin daina biyansu albashin ne dama domin a horar da su.

“Ba za su samu nasara ba domin mun samu wasu hanyoyi na ciyar da iyalanmu. Da yardar Allah ko ba albashi za mu yi rayuwa. Don haka in sun ga dama su daina biyanmu na wata biyar, ba za mu daina yajin aikin ba sai an biya mana bukatunmu,” inji shi.

Wani malami a Jami’ar Jihar Taraba da ba ya so a ambaci sunansa ya ce ba karamar wahala suke sha ba kan rashin biyansu albashi, inda ya ce wasunsu sun koma noma, wasu na kiwo wasu kuma sun koma amfani da motocinsu suna daukar fasinja domin samun na abinci.

“A wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa a ce mutum ya kwashe kusan wata hudu ba albashi, ai dole a shiga damuwa. Don haka nake so gwamnati da jagororinmu su zauna su samu matsaya domin mu dawo bakin aiki,” inji shi.

Shi ma wani malami a Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce rashin biyan su albashin ya jefa shi da iyalansa a cikin matsananciyar wahala.

Ya ce yana rayuwa ne da bashin da kuma taimakon da yake samu daga ’yan uwa da abokan arziki, sannan ya kara da cewa da yawansu sun fara sayar da wasu kadarorinsu domin biyan bukatunsu na yau da kullum.

Ya ce “Wasunmu sun sayar da motocinsu, wasu sun sayar da kwamfutoci da wayoyinsu. kungiyar ma’aikata dai tana ba mu bashin kayan abinci.”

Malam Umar Magaji Abubakar ya ce suna cikin wahala matuka kasancewar ana lokacin tsadar rayuwa da ko ana biyan albashin da kyar ake iya daukar dawainiyar yau da kullum.

“Sai dai mun dauki izina na nemo wasu hanyoyin neman na abinci ba tare da tarewa kacokan ga albashi ba,” inji shi.

Malam Abubakar Uba na Jami’ar Kashere cewa ya yi wasu daga cikinsu sun gaji da yajin aikin, sun kosa a dawo makaranta domin su ci gaba da rayuwa.

Wani malami da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce shi kabukabu yake yi da motarsa, “Da yawa daga cikinmu suna cikin kunci da damuwa ta dawainiyar iyali. Ni ina amfani da motata ce wajen kabu-kabu, sannan ita ma matata tana dan taba harkokin kasuwanci,” inji shi.

Wata malama a Jami’ar Legas, Mis Bolajoko DidonOgbechi ta ce sun shiga wahala da damuwa na rashin kudaden biyan bukatun yau da kullum. A cewarta, wasu abokan aikinta sun rasu ana cikin yajin aikin, “Kai kanka ka yi tunani mana yaya rayuwa za ta kasance ba tare da albashi ba, duk da cewa gwamnati ta san aikinmu ba irin na sauran ma’aikata ba ne, muna wasu abubuwan da dama. Muna bincike, muna ayyukan taimakon al’umma.

“Wasu abokan aikinmu biyu sun rasu kwanakin baya. Wasunmu suna fama da rashin lafiya, kuma suna bukatar kudi domin sayen magunguna. Biyan kudin makarantar yaranmu ma kadai ya zama matsala yanzu. Wannan abin da gwamnati take mana zalunci ne,” inji ta.

Shugaba Buhari ya shiga maganar

Aminiya ta ruwaito a makon jiya Shugaba Buhari yana kira ga malaman jami’o’in su tausaya wa daliban da iyaye su dawo bakin aiki, inda ASUU ta mayar masa martani da cewa shi kadai ne zai iya magance lamarin.

A ranar Talata da ta gabata Shugaba Buharin ya ba Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, mako biyu ya kawo karshen yajin aikin na ASUU.

Sannan a wani mataki da ake ganin zai taimaka wajen kawo karshen lamarin, Shugaban ya kuma umarci Ministan Ilimin ya jagoranci zaman sulhun da gwamnati ta gayyaci ASUU don sasantawa da ita da sauran kungiyoyin jami’o’i da ke yajin aiki maimakon Ministan Kwadago Chris Ngige.

Ya kuma ba shi wa’adin mako biyu ya shawo kan duk matsalolin da suka hana sulhu da malaman jami’ar, sannan a kawo masa rahoto.

Mako biyu ba zai yi aiki ba idan – ASUU

A martanin kungiyar ASUU, ta ce wa’adin mako biyu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, na ya kawo karshen yajin aikin da suke yi, ba zai yi tasiri ba idan har aka sa Ministan kwadago Chris Ngige, a cikin sulhun.

Da yake mayar da martani kan wannan umarni a lokacin da yake amsa tambayoyi a wata ganawa da manema labarai a Abuja, Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya nanata cewa Ngige a matsayinsa na “Babban Mai sasantawa” shi ne kuma babban jigon da ke rura wutar rikicin da ake samu a manyan makarantu a fadin kasar nan.

Farfesa Osodeke ya ce, “To, muna addu’ar wannan wa’adi ya yi aiki a wannan karo domin idan za ku tuna, a baya an ba da irin wannan umarni, inda NIREC a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi da kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) suka shiga tsakani. Amma wane sakamako aka samu?”

Farfesa Emmanuel Osodeke ya kuma bayyana cewa ba za su amince da yaudara daga gwamnati ba.

Ya ce ya zamo dole su wayar wa al’ummar Najeriya kai kan halin da ake ciki, wanda ya ce tun farko gwamnati ce ta jawo shi.

Ya ce: “Mu kungiyoyin masu ilimi ne, da tabbatattun hujjoji muke amfani, don haka dole mu sanar da mutane halin da muka rabu da su a duk zamanmu na baya.

“Kada a manta da maganganun da Shugaban kasa da sauran bangarorin Gwamnati suka yi a baya-bayan nan, musamman wadanda Ministan kwadago ya yi cewa babu wata yarjejeniya tsakaninmu da su, da kuma wai mun zauna mun tsara albashinmu ba da su ba, ban da cewa mun bukaci wakilan ma’aikatun gwamnati da hukumomi su cire kansu daga tattaunawar.

“Mun zauna sau da dama da Ministan kwadago, amma babu wani tartibin abu da muka cim ma, sai kwan-gaba kwan-baya. Misali sai ya fito kiri-kiri ya nuna yana goyon bayan a biya mana bukatunmu na shekarar 2009 cikin wata shida, sai kuma ya zo da wata maganar daban bayan nan.

“Da muka bayyana masa damuwarmu kan yadda tattaunawar ke tafiyar hawainiya, sai ya bude baki ya ce shi fa ba shi ya dauke mu aiki ba, mu tafi ga Ministan Ilimi shi ne ya fi dacewa da sabgarmu,” inji shi.

Kungiyar NLC da ta Sufurin Jirgin Sama za su yi zanga-zangar goyon bayan ASUU

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta ce za ta gudanar da zanga-zanga a ranakun 26 da 27 ga watan Yulin 2022 don nuna goyon bayanta ga yajin aikin.

Shugaban NLC na kasa, Kwamared Ayuba Wabba ne ya bayyana haka a cikin wata wasika da ya sa wa hannu tare da Sakataren kungiyar, Mista Emmanuel Ugboaja, kuma aka raba wa shugabannin kungiyar na jihohi.

A cewar Kwamared Ayuba, daukar matakin ya zo daidai da shawarar Kwamitin Zartarwar kungiyar ta kasa, wanda ya gudanar da taro ranar 30 ga watan Yuni.

Kungiyar kwadagon dai ta ce za ta yi zanga-zangar ce don tilasta wa Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su yi abin da ya dace don kawo karshen yajin aikin.

Kwamared Wabba ya ce, “Mun shirya wannan zanga-zangar ce don ganin ’ya’yanmu sun samu sun koma makarantun gwamnati da kuma inganta harkar ilimi.

“Za a yi wannan zanga-zangar ce a ranakun 26 da 27 a dukkan jihohin Najeriya da kuma Abuja. Wuraren da za a fara zanga-zangar su ne Sakatariyar NLC da ke jihohin da kuma ta kasa da ke Gidan kwadago a Abuja,” inji shi.

A nasu bangaren, kungiyar Ma’aikatan Jiragen Sama ta Najeriya (ANAP) ta yi barazanar fita zangazanga tare da kungiyar kwadago a ranar 26 da 27 ga watan Yuli, don nuna goyon bayanta ga yajin aikin.

Cikin wata sanarwa da Babban Sakatarenta na kasa, Abdulrasak Sa’idu ya fitar a ranar Litinin, kungiyar ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen yajin aikin malaman jami’ar cikin gaggawa.

Ya ce yajin aikin kungiyar ba abin da ya haifar ga kasar nan face munanan dabi’u ga dalibai matasa da ba su da abin yi, wadanda hakan ka iya zamowa barazana ga rayuwarsu a gaba.

Haka kuma sanarwar ta ANAP ta ce yajin aikin na nuna mawuyacin halin da bangaren ilimi ke ciki a Najeriya, wanda hakan abin kunya ne ga shugabanninta.

“Yanzu fa ana maganar shafe wata hudu ana yajin aikin, kawai saboda gwamnati ta yi kememe ta ki cika alkawarin da ta dauka, ya kamata a ce ta kawo karshensa da ma na kungiyoyin NASU da SAUTHRIAI da NAAT,” inji shi.

Haka kuma kungiyar ta ce yajin aikin ba wai iya ’ya’yan kungiyar ASUU ke wahala saboda shi ba, har ma da iyaye da al’umma, ban da matsalar tattalin arziki da ya leka kowane gida.

Haka ANAP ta ce ilimi jigon ci gaban kowace al’umma ce, wanda ke kai ta ga babban mataki a idon sauran kasashen duniya, kuma yin shakulatin bangaro da lamarinsa abu ne da za a yi da na sani kan sa a gaba.