✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan adawa ne suka sa aka kona kadarori na – Tinubu

Ana maye gurbin dukiya da aka rasa amma shi rai in an rasa shi ba a iya maye gurbinsa.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jagora a jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya ce masu adawa da shi a siyasa ne suka dauki nauyin wadanda suka lalata masa dukiya a lokacin rikici ya biyo bayan zanga zangar #ENDSARS.

Bola Tinunbu ya bayar da shaidar haka ne a makalar da ya gabatar  a ranar Lahadi mai taken zanga zangar #ENDSARS da darasun da ya kamata gwamnatin dimokuradiyya ta koya.

Ya ce yayi takaicin yadda maharan suka sauke mugun nufinsu a kanshi, a yayin da ya mallaki kaso mafi yawa na kafar yada labarai na gidan Talbijin na TVC da kamfanin Jaridar ‘The Nation’ wadanda maharan suka kone.

“Amma na gode wa Allah da ya kasance ba a illata wani daga ma’aikatan ba.

“Ana maye gurbin dukiya da aka rasa amma shi rai in an rasa shi ba a iya maye gurbinsa”, inji shi.