✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Arewa ku kare kanku daga ’yan ta’adda —CNG

CNG ta sake kira ga jama’ar Arewa da su tashi su kare kansu daga ’yan ta’adda.

Kungiyar al’ummar Arewa (CNG) ta sake kira ga jama’ar yankin da su tashi su kare kansu daga ’yan ta’adda.

CNG ta yi kiran ne bayan kisan da Boko Haram ta yi wa wasu manoma a garin Zabarmari da ke Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno.

Kakakin kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce ba za a sake dogaro da dakarun Gwamnatin Tarayya don kare al’ummomin Arewa ba.

Suleiman, wanda ya ce halin da ake ciki yanzu ba “abin jurewa ba ne”, ya bukaci a yi wa shugabancin sojojin kasar da dukkan kadarorin tsaro garambawul nan take.